An haifi Jean Luc Melanchon ne a 1951 a garin Tanger na Morocco, ya yi karatunsa ne a fannin falsafa da nahawun zamani. Dan gurguzu ne a 1986 ya zama sanatan faransa mafi kankantar shekaru.
Ya shugabanci bangaren masu tsarin ra’ayi na jam’iyar gurguzu ta PS, inda ya yi kokowar nuna adawa da bin sahun yan social-démocratie na turai.
Bayan nasarar da bagaren masu sassaucin ra’ayi na yan gurguzu ya fice daga jam’iyar ta Socialiste PS 2008 inda ya kafa tasa jam’iyar bagaren hagu Front de Gauche. A karkashinta ya zama dan majalisar dokoki 2009, an sake zabensa a 2014.
Ya yi takarar kujerar shugabancin kasar Faransa a zaben 2012, inda a zagayen farkya samu yawan kuri’un miliyan 4 (11,1 %).
A watan fabrairun 2016, Melanchon ya sake gabatar da takarasa a zaben shugabancin kasar 2017 inda a zagayen ya hada kan kuriu miliyan 7 20%. Ya zama dan majalisar dokoki dake wakiltar yankin Bouches-du-Rhône, à Marseille, da kimanin 60% na kuriun da aka kada
Marubuci ne da ya rubuta litattafa 19 daga ciki a kwai « l’Ere du peuple », wanda ya sayar da duban kofi inda yake ilimatar da yadda al ‘umma ya kamata ta bijire
Jean-Luc Melanchon ya samu babbar lambar karamawa ta kasar Argentina.
Yanzu kuma ya sake gabatar da takararsa a zaben shugabancin kasa na 2022 da za a gudanar a ranar 24 ga wannan wata na Avrilu a karkashin tarayyar al’umma.
A wani labarin an daban kuma Tsohon Gwamnan Jihar kano dake Najeriya Rabiu Musa Kwankwaso ya kawo karshen zamansa a cikin Jam’iyyar PDP sakamakon sanarwar da yayi na ficewa daga cikin ta.
Tsohon gwamnan ya ce sakamakon wasu dalilai na rashin fahimtar juna, ya yanke hukuncin ficewa daga jam’iyyar daga yau Talata, 29 ga watan Maris na shekarar 2022.
Kafin dai wannan lokaci an dade ana rade radin cewar Kwankwaso zai sauya sheka zuwa Jam’iyyar NNPP domin tsayawa takarar zaben shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Tuni wasu daga cikin magoya bayan sa suka fice daga PDP domin komawa sabuwar Jam’iyyar a Jihar Kano da kuma wasu jihohi dake cikin kasar.