A Najeriya akalla mutane 27 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-hare da mayakan ISWAP suka kaddamar kan garuruwa da dama da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin kasar cikin makon da ya gabata.
Guda cikin jagororin mayakan sa kai da ke sanarwa da kamfanin dillancin labaran Faransa yadda farmakin ya gudana, ya ce ‘yan ta’addan na ISWAP na zargin fararen hular kauyukan 3 da taimakawa Sojin Najeriya a yakin da suke yi da ayyukan ta’addanci.
Tun a shekarar 2016 kungiyar Boko Haram ta rabu gida biyu inda tsagin ISWAP ke biyayya ga kungiyar IS tare da fadada hare-hare kan jami’an tsaro da kadarorin gwamnati.
Jami’an tsaron yankin dai sun ki bayyana AFP masaniyarsu game da farmakin na ranar juma’a da ya shafi kauyukan Sabon garin Kimba da Madara Girau da kuma Ngama dukkaninsu gab da gandun dajin Sambisa.
Acewar wasu ganau mayakan sun rika shiga kauyukan daya bayan daya suna zabar mutanen da suke yiwa yankan rago wadanda suka zarga da taimakawa dakarun Soji.
A wani labarin na daban Ma’aikatar tsaron Najeriya tace dakarun kasar sun yi nasarar kashe mayakan boko haram da ISWAP sama da 120 a cikin makwanni 3 sakamakon hare haren da suke kai musu a yankin arewa maso gabashin kasar.
Janar Onyeuko yace kwamandodin ISWAP da dama sun mika wuyar su ga sojojin Najeriya cikin su harda shugaban su da kuma wasu mayakan da suka fito daga kasashen ketare dake samar musu na na’urorin fashewa wadanda aka hallaka sakamakon harin sama.
Daraktan yace mayakan da suka mika kan su ga sojojin tare da iyalan su sun kai 965, kuma 104 daga cikin su suna kungiyar ISWAP ne, yayin da aka kuma kubutar da mutane 25 da suka yi garkuwa da su.
Janar Onyeuko yace sun tantance mayakan da suka mika kan su, kuma sun mikawa hukumomin gwamnatin da suka dace domin daukar mataki akan su.
Bayan wadanda suka mika kan su, sojojin sun kuma kama Yan ta’adda 50 a wurare daban daban tare da motocin dake dauke makaman hari guda 5 da tarin alburusai.
Daraktan ya kuma sanar da nasarar da sojojin suka samu a yankunan jihohin Adamawa da Yobe.