Sabon ministan ilimi mai zurfin gwamnatin Taliban Abdul Baqi Haqqani ya ce za a bai wa mata a Afghanistan damar shiga jami’o’i amma bisa sharadin ba za su cakudu da maza ba.
A farkon wannan wata kungiyar Taliban ta sanar da cewa mata na da damar karatu a jami’a idan suka kiyaye sharadin sanya rigar abaya da nikabi.
Kungiyar Taliban dai tayi ikirarin nisanta kan ta da tsauraran manufofin da ta runguma a zamanin mulkin ta na farko fiye da shekaru 20 da suka gabata.
A wani labarin na daban ayakan Taliban sun tarwatsa dandazon matan da ke zanga-zangar kin jinin Pakistan a birnin Kabul na Afghanistan inda mayakan suka rika harbi a iska wanda ya kai ga tarwatsa taron matan wadanda suka taru a yankuna daban-daban na birnin.
Akalla mabanbantan zanga-zanga 3 mata suka jagoranta a birnin na Kabul yau talata inda su ke kalubalantar salon mulkin Taliban na shekarun 1996 zuwa 2001 lokacin da kungiyar ta rika zartas da hukuncin kisa kan wadanda aka samu da laifi yayinda aka rika yanke hannun barayi.
Guda cikin masu zanga-zangar wadanda suka yi dandazo a farfajiyar ofishin jakadancin Pakistan da ke Kabul wadda ta bayyana sunanta da Sarah Fahim ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa matan Afghanistan sun gaji da yaki, suna bukatar a gina musu kasarsu suna bukatar zaman lafiya tare da cikakken ‘yanci.
Masu zanga-zangar sun zargi Pakistan da kitsa yadda lamurra ke tafiya a kasar musamman bayan ziyarar shugaban sashen leken asirin kasar Faiz Hameed a Kabul cikin karshen mako.