Masar Za Ta Janye Sojojinta Daga Cikin Tawagar MDD Dake Mali.
Tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, a kasar Mali, ta sanar da shirin kasar Masar na janye sojojinta daga cikin tawagar daga ranar 15 ga watan gobe har sai abunda hali ya yi.
Wannan dai a cewar Minusma na da nasaba ne da yawaitar hare haren da ake kai wa tawagar.
A farkon wannan makon ne Masar, ta bayyanawa MDD, damuwarta game da yawan hare haren da ake kaiwa sojojinta.
Tun daga watan Maris na sojojin Masar shida ne suka rasa rayukansu a hare haren kwantan bauna uku da aka kai da ababen fashewa kan ayarin motoci dakarun na MDD.
Baya ga su ma da akwai wasu 15 da suka jikkata ciki har da masu munanen raunuka.
READ MORE : Nijar Da EU Sun Cimma Sabuwar Yarjejeniyar Yaki Da Safarar Bakin Haure.
Masar na da kimanin dakaru 1,000 a Mali, daga cikin dubu uku da take da su a cikin tawagogin wanzar da zaman lafiya a Afrika.
READ MORE : Iran Ta Kaddamar Da Sabon Sashen Ruwa Na Jiragai Marar Matuka.
READ MORE : Marcus: Saudiyya Bata Damu Da Halin Da Falasdinawa Suke Ciki Ba.
READ MORE : Kashshogi: Shugban Amurka Ya Tuhumi Muhammad Bin Salman Na Saudiyy.