Masar; An Fara Taro Na 3 Dangane Da Kundin Tsarin Mulki Na Kasar Libya.
An fara taro na 3 dangane da kundin tsarin mulkin kasar Libya a birnin Alkahira na kasar Masar.
Kamfanin dillancin labarin ISNA na kasar Iran ya bayyana cewa rashin zaman lafiya da kuma rashin hadin kai tsakanin jami’an gwamnatoci biyu masu iko da kasar Libya ya sa, kasar take cikin zamna dardar a ,afi yawan lokata.
Labarin ya kara da cewa a halin yanzu dai za’a ci gaba da taron tantance makoman sabon kundin tsarin mulkin kasar don sanin makamarsa.
Wakilin MDD na musamman kasar kasar Libya Estefan Williams ya sami halattan taron sannan a jawabin da ya gabatar ya bukace bangarorin ‘yan siyasa na kasar Libya su rumgumi tattaunawa don ita ce kadai hanyar dawo da zaman lafiya a kasar.
READ MORE : Iran; ‘Yan Majalisar dokoki Sun Ce IAEA Da Shugabanta Sun Rasa Mutunci Saboda Nuna Bambanci.
Kasar Libya dai ta fada cikin tashe-tashen hankula ne tun shekara ta 2011 a lokacin yan tawaye masu samun goyon bayan kasashen yamma suka kifar da gwamnatin kasar.
READ MORE : PSG Ga Gab Da Kulla Kwantiragi Da Zidane Don Maye Gurbin Pochettino.
READ MORE : Shugaban Majalisar Dokokin Kasar Iraqi Ya Amince Da Murabus Na Wakilan Sadr.