Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool za ta hadu da Manchester City a wasan gab da na karshe na cin kofin FA bayan nasararta ta lallasa Nottingham Forest a jiya lahadi da kwallo 1 mai ban haushi.
A bangare guda Crystal Palace da ta yi nasara kan Everton da kwallaye 4 da nema za ta hadu da Chelsea wadda a asabar din da ta gabata ta lallasa Middlesbrough da kwallaye 2 da nema.
Liverpool wadda ta lashe kofin Carabao a wannan kaka na harin kofin na FA ne karo na 4 yayin da Manchester City jagorar firimiya ke harin kofin karo na 3.
Wasannin na gab da karshe dukkaninsu za su gudana ne a filin wasa na Wembley da ke London tsakanin ranakun 16 zuwa 17 ga watan Aprilu, wato kwanaki kalilan bayan Manchester City ta karbi bakoncin Liverpool a firimiyar ingila, kungiyoyin da suka juye zuwa manyan abokanan dabi a yanzu.
Kungiyoyin biyu da yanzu haka ke da tazarar maki 1 tal a tsakaninsu matsayin jagora da mai bi mata a teburin firimiya na tseren lashe kofuna 3 ne wannan kaka da suka kunshi na firimiyar da na zakarun Turai da kuma FA wanda kuma dukkaninsu za su iya bayar da mamaki.
A wani labarin na daban Shugaba Joe Biden na Amurka na shirin kai ziyara Poland a juma’a mai zuwa inda gana da shugaba Andrzej Duda don tattaunawa kan mamayar Rasha a Ukraine.
A cewar sanarwar mai dauke da sa hannun kakakin fadar White House Jen Psaki ta ce Biden zai gana shugabancin NATO da na G7 da kuma EU gabanin ziyarar a Poland, don tattauna yadda za su bullowa Rasha a abin da ya kira zaluncin da ta ke aikatawa a Ukraine.
Psaki ta ce za su ci gaba da jan hankalin Duniya don ganin sun ci gaba da samun goyon baya ga al’ummar Ukraine tare da sukar shugaba Vladimir Putin na Rasha.
Sai dai Psaki ta ce ziyarar ta Biden ba ta da shirin kai shi zuwa Ukraine don ganewa idonsa yakin, sabanin shugabannin Poland da Czech da kuma Slovakia da suka je har Kyiv don ganewa idonsa yadda yakin ke gudana.