Mali ta zargi sojojin Faransa da yi mata leken asiri a lokacin da suka yi amfani da wani jirgi mara matuki wajen daukar hoton abin da Faransa ke zargin sojojin haya ne ke binne gawarwaki a kusa da wani sansanin soji.
Kwana daya da faruwar hakan, sojojin Faransa sun watsa wani faifan bidiyo da ta ce ya nuna sojojin hayar Rasha suna rufe gawarwaki don zargin sojojin Faransa da suka fice da aikata laifin.
Da sanyin safiyar Talatar nan ne dai rundunar sojojin Mali ta sanar da gudanar da bincike kan gano wani kabari da aka yi a sansanin na Gossi.
Rundunar ta ce ta gano kabarin ne washegarin da aka wallafa hotunan.
Mali dai ta zargi Faransa da yin leken asiri da kuma yunkurin bata sunan sojojin ta da bidiyon da aka dauka da jirgi mara matuki.
Kakakin gwamnatin kasar Abdoulaye Maiga ya ce, anyi amfani da jirgin maras matuki ne domin yin leken asiri ga dakarun sojin Mali.
A wani labarin na daban Gwamnatin Jihar Zamfara da Najeriya ta sanar da sauke manyan Sarakunan Jihar guda biyu da Magajin Gari guda saboda samun su da hannu wajen ayyukan ta’addancin da suka addabe ta.
Sanarwar dake dauke da sanya hannu Zailani Bappa, mai magana da yawun gwamnan tace an kuma sauke Suleiman Ibrahim Danyabi a matsayin Magajin Garin Birni Tsaba.
Sanarwar tace an dauki matakin sauke Sarakunan ne bayan taron majalisar zartarwa wanda Mukaddashin Gwamnan Jihar Hassan Nasiha ya jagoranta wanda ya amince da shawarwarin wani kwamitin bincike da ya gano hannun wadannan Sarakuna cikin matsalar tsaron da ta addabi jihar.
Kafin dai wannan lokaci an dakatar da wadannan Sarakunan daga aiki saboda zargin da ake musu.