Kakakin ma’aikatar tsaron Mali bai musanta wannan yunkuri ba, sai dai yace ya zuwa wannan lokaci babu wata yarjejeniyar da aka kulla.
Wannan yunkuri na iya haifar da matsalar dangantaka tsakanin Faransa da Mali, musamman ganin yadda Rasha ke fadada ikon ta a yankin.
Tun daga shekarar 2013 kasar Faransa ta tura dubban sojojin ta tare da jiragen yaki Mali da kuma Yankin Sahel domin yakar ‘Yan ta’addan dake alaka da Al Qaeda da kuma kungiyar IS.
Dangantaka tsakanin Faransa da sojojin dake iko a Mali ta tabarbare a watan Agustan bara sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya kaiga kifar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keita.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana bacin ran sa da tsaikon da aka samu wajen gudanar da zabe da kuma mayar da mulki ga fararen hula tare da sakin ‘yan ta’addan da aka tsare da su a matsayin musaya da mutanen da akayi garkuwa da su.
A watan Yunin da ya gabata, Faransa ta dakatar da hadin kan da take yi na soji da Mali, yayin da shugaba Emmanuel Macron ya bayyana shirin rufe wasu sansanonin sojin Faransa dake kasar.
Daukar sojojin hayar da Mali ke shirin yi ya na iya kawo karshen taimakon sojin da Faransa ke baiwa kasar da kuma kwashe dakarun ta daga Mali zuwa Nijar.
Dama dai ana ganin zaman sojojin kasashen yammacin turai a kasashen afirka bashi da wata fa’ida, musamman ga kasashen na nahiyar afirka.