Al’ummar kasar Mali sun gudanar da gamgani ranar Asabar a birnin Bamako domin murnar ficewar sojojin Faransa daga kasar Mali, a wani yunkuri na nuna goyon baya ga mahukuntan rikon kwaryar da sojoji suka mamaye.
Sai da gangamin bai hada mutane sosai kamar yadda aka gani a baya ba, wato yayin zanga-zangar goyan bayan juyin mulki da sojoji sukayi sai biyu a watan Agusta shekarar 2020 sannan a watan Mayu 2021, inda dubban mutane suka taru a Bamako.
Makomar dakarun Majalisar Dinkin Duniya
Faransa da kawayenta na Turai sun tsara janyewar sojojinsu daga Mali a ranar Alhamis, lamarin da ya sa sauran kasashen ketare suka fito fili suka nuna shakku kan kudurinsu, da kuma tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali (Minusma) ke nazari kan tasirin wannan janyewar.
Watsi da shirin zabe
Gwamnatin mulkin soji a Mali ta yi watsi da alkawarin da ta dauka na gudanar da zabe a watan Fabrairun 2022 domin komawar farar hula kan karagar mulki. Ta yi kira da a samar da sauye-sauye mai zurfi tare da jajircewa kan ikon mallakar kasa tun bayan da kasashen Afirka ta Yamma suka kakabawa Mali takunkumi mai tsanani na tattalin arziki da diflomasiyya a ranar 9 ga watan Janairu.
wani labarin na daban AKungiyar Tarayyar Turai EU ta sanya sunayen ‘ya’yan shugaban kasar Rasha Vladimir Putin mata biyu da wasu mutane sama da 200 cikin bakin kundi, a wani bangare na sabon takunkumin da ta laftawa kasar Rashan sakamakon mamaye Ukraine da take cigaba da yi.
A jumlace dai kimanin ‘yan Rasha da masu alaka da su 217, kungiyar EU ta sanya sunayensu cikin bakin kundinta.
Dangane da ‘ya’yan shugaba Putin kuwa, da suka hada da Maria Vorontsova da Katerina Tikhonova, tuni dama Amurka da Birtaniya suka sanya musu takunkumi.
Mahaifiyar yaran ita ce tsohuwar matar shugaban Rasha Lyudmila, wadda aka sanar ta rabu da Putin a cikin shekarar 2013.