A cikin wannan biki, babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya jinjina ga sakon hikima na Ayatullah Makarim Shirazi, inda ya yi ishara da ranar zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci, yana mai cewa: Wasu sun yi imani da faruwar lamarin juyin juya halin addini abu da bai yiwuwa ba, suna masu kudirce cewa gyara sannu a hankali shine zai fi, amma sai ga shi juyin juya halin Musulunci mai daukaka ya faru a matsayin abin al’ajabi na mu’ujizar wannan karni.
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: A cikin wannan biki, babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya jinjina ga sakon hikima na Ayatullah Makarim Shirazi, inda ya yi ishara da ranar zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci, yana mai cewa: Wasu sun yi imani da faruwar lamarin juyin juya halin addini abu da bai yiwuwa ba, suna masu kudirce cewa gyara sannu a hankali shine zai fi, amma sai ga shi juyin juya halin Musulunci mai daukaka ya faru a matsayin abin al’ajabi na mu’ujizar wannan karni kuma ya canza ma’auni na siyasa da nau’oi masu fuskantar juna.
Ayatullah Ramezani ya ce game da sharuddan masu bincike na Wiki na Shi’a: Dole ne wannan kundin ya zama na zamani; A daya bangaren kuma, ya zama wajibi mashigar Shi’a Wiki ya dace da wuraren da aka yi niyya domin gabatar da koyarwar Ahlul Baiti (AS) ga duniya.
Da yake yaba da kokarin jami’an ma’aikatar ilimi da al’adu na majalisar Wiki Shi’a da Encyclopaedia, Malamin Manyan Hauzozin Ilimi ya ce ga manyan ma’aikatun wannan fanni: Na yaba da hadin kai da juyi da canji da ke akwai a cikin Wiki Shi’a da kuma gagarumin kokarin jami’an da suka gudanar da aikin bisa ga manufofin da aka sanar.
A yayin da yake bayani kan manufofi da hadafofi Wiki-Shia, ya bayyana cewa wajibi ne a gabatar da ilimin addini a cikin tsari da kudnin masaniya, sannan ya kara da cewa: Saboda addini tarin koyarwa ne da koyarwar da ke da alaka ta kut-da-kut da madaidaicin hankali, don haka Ruhin Wiki-Shia ya kamata ya zama addini na hankali.
Babban Shugaban Majalisar Ahlul-Baiti (AS) Ta Duniya ya ga ya dace a mai da hankali kan yadda ake gabatar da koyarwar Shi’a yana mai cewa: Malaman Musulunci da malaman duniyar Shi’a sun bar wani tarihi mai daraja da ya kamata a gabatar da su. Bude sabbin kafofin “Wiki Turath” da “Shia Data” da nufin gabatar da koyarwar Shi’a, wadannan ayyuka guda biyu masu muhimmanci ne kuma manya-manyan ayyuka kuma an gudanar da aiki mai kima sosai.
Source: ABNAHAUSA