Dakarun Burkina Faso 11 ne suka rasa rayukan su biyo bayan wani harin mayakan jihadi a jiya alhamis a gabashin kasar. Majalisar sojin kasar na iya kokarin shawo kan wannan matsalar mayakan jihadi a Burkina Faso.
A dan tsakanin nan kasar ta Burkina Faso ta fuskanci hare-haren mayakan jihadi, al’amarin dake neman durkusar da sha’anin tsaro ga baki daya a wannan yanki.
Rashin tsaro na daga cikin matasalolin da suka yi awon gaba da tsofuwar gwamnatin tsohon Shugaban kasar Christian Kabore da aka yiwa juyin mulki,duk da kokarin kungiyar G5 Sahel a lokacin.
Rashin kayan aiki da horo da ya dace suka tilastawa majalisar sojin kasar sake gayyato tsofin sojojin kasar a wannan yaki da yan ta’adda.
Abba Seidk masanin harakokin siyasa da zamantakewar kasashen yammacin Afrika ya bayyana yada yake kalon wannan al’amari.
A wani labarin na daban wani kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya ce sojojin Mali sun hana dakarunsu sintiri a tsakiyar garin Djenne, yankin da ake fama da tashe-tashen hankula da kuma hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi a yankin Sahel.
Wannan al’amari dai ya zo ne makwanni kalilan kafin muhawarar da Majalisar Dinkin Duniya za ta yi a kan ko za ta sabunta wa’adin aikinta na wanzar da zaman lafiya.
Wani mai magana da yawun rundunar Minusma, Olivier Salgado, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, “Abin takaicin shi ne, yadda sojojin Mali suka hana ‘yan sandan Majalisar Dinkin Duniya yin sintiri da aka shirya gudanarwa a ranar Litinin 16 ga watan Mayu, bisa hujjar cewa ana gudanar da ayyukan soji a yankin.
Sai dai Kanar Karim Traore, kwamandan sojojin Mali na shiyyar yankunan Mopti da Djenne, ya ce Mali ba ta kawo cikas ga ayyukan Majalisar Dinkin Duniya ba, kuma an dage aikin sintirin da dakarun Majalisar Dinkin Duniya za su yi ne kawai, ba haramtawa ba, saboda ayyukan sojin da ke gudana.
A farkon wannan shekarar ne dai gwamnatin mulkin sojan kasar Mali ta kafa dokar hana zirga-zirgar jiragen sama a wani babban yankin kasar lamarin da ya dagula ayyukan Majalisar Dinkin Duniya.
Har yanzu kuma rundunar majalisar ta Minusma na jiran izinin shiga garin Moura, a tsakiyar kasar ta Mali, inda kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Rights Watch ta ce sojojin Mali da sojojin haya na Rasha sun kashe fararen hula 300 a watan Afrilu.