Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kazamin harin ta’addancin da ya hallaka sojin kasar Mali kusan 30 a Mondoro dake tsakiyar kasar.
Wakilin ya dada jaddada aniyar rundunar MINUSMA ta Majalisar wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin Mali.
Rundunar sojin Mali tace sojoji 27 suka mutu, yayin da wasu 33 suka samu raunuka sakamakon harin Yan ta’addan.
A wani labarin na daban Gwamnatin Mali ta musanta zargin da ake yi wa sojojinta na yi wa fararen hula da dama kisan gilla a yankin tsakiyar kasar a farkon watan Maris.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta a wannan makon, ya nuna gawarwakin mutane da dama da aka kone su, bayan rufe musu idanu tare da daure hannayensu wuri guda. Wasu daga cikinsu kuma an ga ramuka a bayan kawunansu.
Wani jami’i a a yankin na tsakiyar kasar Mali, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an gano gawarwakin ne a daren ranar Talatar da ta gabata, kuma ana kyautata zaton sune wadanda sojojin Mali suka kama wasu a ranar 20 ga watan Fabrairu, wasu kuma a ranar 1 ga watan Maris.
Sai dai, gwamnati kasar ta yi fatali da zargin, tare da bayyana shi a matsayin karya tsagwaronta.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta sha zargin sojojin Mali da kashe fararen hula da kuma wadanda ake zargin mayakan sa kai ne a tsawon shekaru goma da suka shafe suna yaki da kungiyoyin da ke da alaka da Al Qaeda da kuma IS.