Jiran da aka shafe tsawon lokaci ana yi domin sanin makomar fitaccen dan wasan kungiyar PSG Kylian Mbappe mai yiwuwa na gaf da karewa, idan har komai ya faru kamar yadda aka za ta a tsakanin zakarun na gasar League 1 ta Faransa da kuma Real Madrid da ke Spain.
Wannan ne dai karo na farko da kungiyar Real Madrid wadda ke karkashin jagorancin Florentino Perez ke gaf da cimma burin ganin Mbappe sauya sheka zuwa gareta, bayan kokarin da tayi har sau biyu a baya, wadanda shugaban Paris Saint German Nasser Al-Khelaifi yayi watsi da su.
Rahotanni sun ce a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, tattaunawa ta yi nisa a tsakanin Madrid da PSG, inda ake sa ran zuwa ranar Juma’a mai zuwa za a kulla yarjejeniya mai cike da tarihi tsakanin Mbappe da zakarun gasar La Liga.
Idan har sauyin shekar Mbappe ta tabbata, wasu majiyoyi sun ce dan wasan zai karbi tsakanin Yuro miliyan 60 zuwa 80 a matsayin ladan kulla yarjejeniya da shi, mai yiwuwa kuma albashinsa da ka iya kaiwa Yuro miliyan 25 a duk shekara.
A wani labarin na daban Kylian Mbappe ya yi alkawarin ba zai rabu da Paris Saint-Germain zuwa Real Madrid ba, a yayin hada-hadar kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu da ke shirin budewa.
Kalaman dan wasan na zuwa ne a yayin da ya rage watanni 6 yarjejeniyarsa ta kare da PSG, inda ake sa ran zai sauya sheka zuwa Real Madrid, kungiyar da ya dade yana fatan komawa.
Tun a watan Agustan da ya gabata Madrid ta yi wa PSG tayin biyanta makudan kudaden kan matashin dan wasan na Faransa mai shekaru 23, amma Paris Saint Germain din ta yi fatali da tattaunawa kan cinikin.
A cikin watannin Fabarairu da Maris za a kara tsakanin PSG da Real Madrid a zagayen gasar cin kofin Zakarun Turai na biyu, kuma yayin tsokaci akan wasan, Mbappe ya ce ba shi da wani buri da ya wuce lallasa Madrid, kungiyar da ake sa ran zai koma nan da ‘yan watanni.
Duk da kashe makudan kudade wajen sayen ‘yan wasa dai, har yanzu PSG ta gaza samun nasarar lashe kofin gasar Zakarun Turai, inda a shekarar 2020 ta yi kusa da samun nasarar, amma ta sha kaye da 1-0 a wasan karshe da ta fafata da Bayern Munich.