Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya karbi bakuncin takwarorinsa na Afirka, a daidai lokacin da alamu ke nuna da cewa Faransa na shirin janye dakarunta da ke yaki da ayyakan ta’addanci daga kasar Mali.
Bayan ganawa da shugabannin kasashen na Afirka, gobe alhamis Macron zai wuce zuwa birnin Brussels domin halartar taron Kungiyar Tarayyar Afirka ta Tarayyar Turai wanda zai share tsawon kwanaki biyu.
Tun shekara ta 2013 ne dai Faransa ta tura dakarun domin yaki da ayyukan ta’addanci a Mali, to sai dai har yanzu akwai gagarumar fargaba dangane da makomar tsaro a yankin, tare da yiyuwar yaduwa ayyukan ta’addanci zuwa sauran kasashen da ke gabar teku.
Lura da wannan matsala ce, Faransa da sauran kasashen Turai suka yanke shawarar kafa sabuwar runduna mai suna Takuba da za ta maye gurbin Barkhane, shirin da ga alama bai samun goyon bayan sabbin magabantan birnin Bamako ba.
A wani labarin na daban Mai horas da Kano Pillars Bafaranshe Emmanuel Lionel Soccoia ya ajiye aikinsa watanni 5 bayan kulla yarjejeniyar shekara 1 da kungiyar a watan Oktoban shekarar 2020.
Lionel ya ce yanzu haka yana bin kungiyar ta Pillars albashin watanni 5 da yawansa ya kai dalar Amurka dubu 25. Zalika ya koka kan gazawar da kungiyar tayi wajen sama mishi takardar izinin zama domin aiki a Najeriya kamar yadda doka ta tsara, abinda ya sa ofishin jakadancin kasarsa Faransa ya nemi ya koma gida, kasancewar cigaba da zamansa a Najeriya ya saba ka’ida.
Sai dai jami’in hulda da kafafen yada labaran kungiyar ta Pillars Rilwanu Idris Malikawa ya musanta zargin kocin mai murabus na cewar ana yi masa katsalandan.