Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi nasara kan Arsenal da kwallaye 2 da nema a wasansu na daren jiya karkashin gasar Firimiyar Ingila, wasan da ke da matukar muhimmanci ga Reds don ganin ta matsa kaimi ga Manchester City a tseren da suke na kokarin lashe kofin gasar.
A minti na 54 ne Diogo Jota ya zurawa Liverpool kwallonta na farko da taimakon Thiago Alcantara gabanin kwallon Roberto Firmino wanda ya zura bayan sako shi a fili da taimakaon Andrew Robertson.
Jurgen Klopp dai bai fara wasan na jiya da taurarinsa Mohamed Salah da shi Roberto Firmino sai ana tsaka da wasa ne ya sako su, tare da cire Jota da Diaz a kokarinsa na rikita lissafin Arsenal wadda ta doka wasan da cikakken karsashi amma ta yi rashin nasara.
Tuni dai masana suka fara hasashen yiwuwar kungiyar ta iya sake lashe kofin na Firimiya a bana, saboda raguwar makin da ke tsakaninta da Manchester City da kuma yadda ta ke wasanninta da karsashi sai dai ta na da babban kalubale la’akari da yadda ta ke shirin tattaki zuwa Etihad a watan gobe.
Arsenal ta yi ta kai farmaki amma kuma mai tsaron ragar Liverpool Alisson Becker na barar da kwallon, wanda ke nuna a haduwa 3 da kungiyoyin suka yi a baya-bayan nan kungiyar ta London ba ta iya zura kwallo ko guda ba.
Haka zalika cikin wasanni 18 da bangarorin biyu suka hadu da juna, sau 1 tal Arsenal ta yi nasara kan Liverpool da kwallaye 2 da 1 a watan Yulin 2020, inda galibi ko dai ta yi rashin nasara ko kuma canjaras.
Yanzu haka dai Liverpool ta rage tazarar da ke tsakaninta da Manchester City jagorar gasar zuwa maki 1 tal wanda ke matsayin barazana ga tawagar ta Pep Guardiola wadda a watan jiya ke da tazarar maki 9 a makwannin baya.
Wasan na jiya shi ne haduwar kungiyoyin biyu karo na 3 a 2022 kuma dukkaninsu Liverpool ke yin nasara ciki har da guda a karkashin gasar cin kofin kalubale da tuni Reds ta lashe kofin bayan doke Chelsea.