Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, Kwamitin Hadin-guiwa tsakanin Majalisar Wakilan Libya da Majalisar Shata Kundin Tsarin Mulkin Kasar, sun cimma matsaya ta farko kan wasu ayoyin dokar kasar har guda 137.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, mai bai wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya shawara, Stephanie Williams ta bayyana farin cikinta kan yadda bangarorin biyu suka amince da babi na biyu da ke magana kan ‘yanci da kuma wani bangare da ke magana kan karfin shari’a.
Tuni dai Firaministan Libya da Majalisar Dokokin Kasar ta zaba, wato Fathi Bashaga ya ce, wannan tagomashin zai bada damar mika mulki ta hanyar gudanar da zaben da al’ummar kasar suka yi na’am da shi.
A cikin watan Maris ne, Mai bai wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniyar shawarar, ta gayyaci Majalisar Wakilan da Majalisar Shata Kundin Tsarin Mulkin Kasar domin ganin sun zabi mambobi shida-shida a tsakaninsu da za su kasance wakilai a cikin kwamitin na hadin guiwar da aka dora wa alhakin tsara kundin tsarin mulkin kasar ta Libya.
Rudanin siyasa
Siyasar Libya dai ta shiga rudani a cikin watan Disamba sakamakon wargajewar shirin gudanar da zabe, inda bangarorin da ke adawa da juna suka yi ta yi wa juna zagon-kasa.
A bangare guda, a Talatar da ta gabata, an ji karar harbe-harben bindiga a babban birnin Tripoili a daidai lokacin da Firaminsta Bashaga ya yi yunkurin kifar da gwamnatin abokin adawarsa kuma Firaminista mai rikon kwarya Abdulhamid Dbeibah, lamarin da ke dada barazanar kazancewar rashin zaman lafiya a kasar wadda tuni yaki ya daidaita ta.
A wani labarin na daban wamnatin ‘yan adawar Libya da majalisar gabashin kasar ta kafa, ta gudanar da zamanta na farko don kalubalantar gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan majalisar dinkin duniya da ke Tripoli.
Kasar ta Libya da ke fama da rikici, na da gwamnatoci biyu ne a cikin ta tun a watan Fabuwairu, inda majalisar kasar ta ambata tsohon ministan harkokin cikin gida Fathi Bashagha a matsayin sabon fara ministan kasar.Nadin nasa dai na zuwa ne a matsayin adawa da na Abdulhamid Dbeibah wanda majalisar dinkin duniya ke goya baya.
A lokacin taron da tsagin Bashagha suka gudanar a ranar Alhamis din nan, sunce suna aikine don sauke nauyin da ya rataya a wuyan su a matsayin su na ‘yan majalisa.
Tsagin gwamnatin da aka samu dai shine na baya-bayannan a kasar a siyasan ce tun bayan faduwar gwamnatin tsohon shugaban kasar Mummer Gaddafi a shekarar 2011.
A dai ranar laraba ce akaji Bashagha na cewa a shirye yake ya yafa aiki a ofishinsa, lamarin da ya fuskanci turjiya daga Abdulhamid ya na mai cewar zai mika gwamnati ne kadai ga zababbiyar gwamnati.
Shi dai Bashagha na samun goyon bayan Khalifa Haftar ne, babban kwamandan da ya jagoranci kwace ikon Tripoli a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020.
Samar da gwamnati biyu a kasar Libya da aka yi a tsakanin shekarar 2014 da kuma 2021 ya kara rura wutar rikicin kasar.