Shugaban Faransa Emmanuel Macron da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen mai tsatsauran ra’ayi za su fafata a muhawarar da za a watsa ta gidan talabijin a yau Laraba, inda kowannensu ke fatan jan ra’ayin masu kada kuri’ar da basu yanke shawarar wanda za su zaba ba.
Wasu zabukan jin ra’ayin jama’a da aka gudanar sun yi hasashen cewar shugaba Macron zai samu nasarar lashe zagaye na biyu na zaben da zai gudana nan da kwanaki 4 da ratar kusan kashi 10 na kuri’un da za kada kan mai tasttsauran ra’ayi Le Pen, wato maimaicin abinda ya faru zaben shekara ta 2017.
Sai dai masu jefa kuri’ar da har yanzu ba su yanke shawara kan inda za su karkata ba ka iya sauya alkaluman.
Bayanai dai sun ce a bana jagorar ‘yan adawa Marine Le Pen ta maida hankali kan shirya wa muhawarar da za ta yi, don kaucewa abinda ya faru shekaru biyar da suka gabata, lokacin da rashin shirinta kan muhawarar ya taka rawa wajen shan kaye da ta sha a hannun shugaba Macron.
Muhawarar kai tsaye tsakanin ‘yan takarar shugabancin Faransa ta kasance al’adar siyasa a kasar tun daga shekarar 1974, lokacin da dan jam’iyyar gurguzu Francois Mitterrand ya yi takara da Valery Giscard d’Estaing. (Valeri Giskar Distar)