Alhamis din nan ne, aka fara aiki da sashin karshe na layin dogo mai tsawon kilomita 2,712, wanda ya zagaye hamada mafi girma a kasar Sin, wato Taklamakan, dake yankin arewa maso yammacin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, bayan da aka shafe shekaru 3 da rabi ana kokarin ginawa.
Sabon sashin layin dogon mai nisan kilomita 825, ya tashi ne daga gabas da birnin Hotan zuwa gundumar Ruoqiang, kusa da gefen kudu da Taklamakan, hamada ta biyu mafi girma a duniya mai cike da yashi, inda kusan kashi 65 na layin dogo yake gudana cikin hamadar.
Bude layin dogo zai baiwa jiragen kasa damar zagaya da’irar hamadar dake zama karo na farko a duniya.
Haka kuma, layin dogon zai saukaka jigilar kayayyaki da tsare-tsaren wasu sana’o’i dake yankin Xinjiang da suka hada da auduga, da dangin gyada, da dabino, da ma’adinai.
A yau, fasinjoji sun yi tattaki zuwa tashar layin dogo da ke birnin Hotan, domin yin balaguro a karon farko a cikin wani jirgin kasa da ke gudun kilomita 120 a cikin sa’a guda, wanda kuma zai taimaka wajen saukaka tafiye-tafiye da inganta rayuwarsu.
Don taimakawa wajen kare hanyar dogon, an gina gadoji guda biyar, inda mafi tsayi daga cikinsu, ya kai fiye da kilomita 18, don daga layin dogon zuwa wani tsayin shinge wanda zai kare shi daga illar guguwar yashi.
A wani labarin na daban shugaban Kamfanin man kasar Rasha, Alexei Miller ya ce za su tsara yadda suke so su sayar da makamashinsu, saboda haka ba sa bukatar katsalandan daga wata kasa domin su suka mallaki dukiyarsu.
Yayin da yake tsokaci dangane da rage yawan iskar gas din da suke tura wa kasar Jamus, Miller ya shaida wa mahalarta taron tattalin arzikin da ke gudana a St.Petersburg cewar, ba sa amfani da dokar da ba su sanya hannu akai ba, saboda haka dole ne kasashen duniya su yi amfani da dokokin da suka shata wa kansu.
A farkon wannan mako,kamfanin Gazprom ya rage yawan iskar gas da yake aika wa kasar Jamus ta bututun ‘Nord Stream’, saboda abin da ya kira gazawar kamfanin Siemens na kammala gyaran tashar daskarar da iskar.
Miller ya ce ya zuwa yanzu babu hanyar warware matsalar da ta taso ta tashar daskarar da iskar, yayin da kamfanin Siemen ya ki cewa komai akan lamarin.
A Alhamis din nan, Kamfanin Gazprom ya ce ya rage tura iskar gas ga kasashen da ba sa cikin Tsohuwar Tarayyar Soviet da kusan kashi 30 daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 15 ga watan Yuni.
Takaddama tsakanin Rasha da kasashen yammacin duniya da ke sayen makamashi daga wurinta, ya yi kamari, saboda matakin da ta dauka cewar dole a rika biyan ta da kudin Ruble maimakon Dala.
Wannan ya sa Rasha ta daina sayar wa kasashen da suka bijire wa matsayinta biyan makamashin da kudin Ruble cikin su har da Poland da Bulgaria da Finland da kuma Netherlands.