Kungiyoyi na fararen hula akalla dubu daya da 500 ne suka bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dage gudanar da taron kasa da kasa kan dumamayar yanayi da ake kira COP26, wanda ya kamata a fara cikin watan nuwamba mai zuwa a birnin Glasgow na kasar Scotland.
Kungiyoyin sun bayyana cewa tsadar allurar kariya daga cutar ta Covid-19 da karancin wannan allura, wadannan abubuwa ne da nuni da cewa zai kasance mai wuya taron ya iya samun nasarorin da ake bukata.
Daga cikin kungiyoyi da suka sanya hannu kan wannan kira, har da Climate Action Network, da Greenpeace, WWF, Action Aide, Oxfam da kuma Amnesty International.
Matukar dai aka ce za a gudanar da wannan taro a cikin watan nuwamba mai zuwa kamar dai yadda aka tsara, wakilai daga kasashe da dama ba za sus amu damar halartar shi ba, wannan kuwa lura da cewa Birtaniya ta wallafa jeri kasashe wasu kasashe da al’ummominsu ba su da izini shiga kasar saboda wannan annoba ta korona.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran Mawazin News ya bayar da rahoton cewa, an fara daukar tsauraran matakan tsaro a kasar Iraki domin tarukan arba’in da za a gudanar.
Rahoton ya ce, a yankin Bagdad jami’an tsaro suna sintiri a cikin gari da kuma cikin dazuzzuka domin tabbatar da cewa babu wasu ‘yan ta’adda da za su kawo barazana ta tsaroa yayin gudanar da tarukan Arba’in.
Baya ga haka kuam sauran yankuna musammanma biranan Karbala da kuma Najaf, tun bayan kammala taruka ashura har yanzu jami’an tsaro suna nan cikin shirin ko ta kwana.
Daga cikin matakan da ake dauka dai kula da layuka na wutar lantarki da kuma layukan butun gas, kamar yadda kuam ake sanya ido a kan dukkanin kai koma na jama’a.
Sannan kuma an kafa kamarori masu daukar hotunan bidiyo a dukkanin yankuna da titina na mayna birane musamman Karbala da Najaf.