Kamar yadda muke samun rahotanni daga garuruwa mabambanta na najeriya yana nuna cewa yanzu haka mambobin harka islamiyya a najeriya karkashin jagoranci Sheikh Ibrahim Zakzaky a sassa daban daban na kasar nan sun fara dukkan shirye shiryen da suka zama wajibi domin gudanar da tattakin ”yaumul arba’in” na bana.
Harakar islamiyya dai ta saba duk shekara takan shirya tattaki a najeriya bisa kowa da wanda ake gudanarwa a karbala ta kasar Iraki kuma wannan tattaki da ake shiryawa a najeriya ya kan samu halartar muliyoyin mutane daga sassa daban daban na najeriya dama makotan najeriya.
Wani abin sha’awa dangane da wannan tattaki shine, ba iya mambobin harkan musulunci wadanda aka fi sani ‘yan shi’a ne kadai suke musharaka ba, har da bangaren ‘yan darika mabiya takarkin ahlul sunna dama kiristoci suma sukan samu halarta kuma ayi tare dasu.
Duk da barazanar da ake fuskanta kowacce shekara ta kwanton bauna gami harin ba zata da jami’an tsaron najeriya bisa umarnin gwamnatin saudiyya sukeyi kuma su dingi yima mambobin na harkar islamiyya aman harkasasi masu rai amma hakan bata taba sanya mambobin na harka Islamiyya sun fasa wannan babbar ibada ta tattaki ba koda kuma da shekara daya ne.
Da yawa a irin wannan hari da jami’an tsaron najeriya kan kawo ma mahalarta wannan taro sun rasa rayukan su, wasu kuma an jikkata su duk dai a sakamakon fitowa ba dauke da makami ba kuma cikin lumana domin nuna juyayi gami da aljihi da kisan jikan manzon Allah Imam Hussain da akayi ranar ashura a filin karbala, shekara ta 61 bayan hijira.
Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin saudiyya bata son wannan tattaki da ake gudanarwa saboda haka take hada baki da wasu gurbatattu daga cikin jami’an gwamnati, inda take basu kudi su kuma sa a aukawa masu ibadar tattakin.
”Jami’an tsaron najeriya da aka dauka aiki domin kiyaye rayuwar mu sune suke kashe mu idan mun fito tattaki, wannan lamari yana mini ciwo matuka” inji wani mamba kuma wanda yake halartar tattakin arba’in