Wani mummunan hari kunar bakin wake wanda shine irin sa na farko tun shekarar 2018, da aka kai birin Peshawar a yankin arewa maso yammacin Pakistan, a wani masallacin mabiya akidar Shi’a, ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 56 sannan wasu 194 suka jikkata.
Harin kunar bakin waken wanda aka kai a gabanin sallar Juma’a, ya bar baraguzan gilasai a kan hanyoyin birnin.
Wannan dai na zuwa ne a ranar farko da aka fara gwajin wasan cricket a Pawalpindi, tsakanin Pakistan da Australia wacce ta kwashe shekaru da dama ba tare da ta ziyarci kasar sabida matsalar tsaro.
Mai magana da yawun gwamnatin lardin Khyber Pakhtunkhwa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa harin na kunar bakin wake ne.
Wani wanda ya shaida harin, Ali Asghar ya ce yaga shigar wani mutum cikin masallacin gabanin sallar Juma’a inda ya ciro karamar bindiga ya fara harbin mutane daya bayan daya.
Babban jami’in ‘yan sandan yankin Muhammad Ijaz Khan, ya shaidawa kamfanin AFP cewa, mutane biyu suka kai harin, kuma ya rutsa da jami’an ‘yan sanda biyu a lokacin shiga masallacin.
A wani labarin na daban Fira Ministan Pakistan Imran Khan ya gargadi majalisar dinkin duniya da cewar rikicin dake tsakaninsu da Indiya kan yankin Kashmir, ka iya kazancewa zuwa barkewar yaki da makaman nukiliya, abinda ba zai yiwa duniya dadi ba.
Fira Ministan na Pakistan yace yanzu haka India ta jibge jami’an tsaro dubu 900,000, a yankin Kashmir mai rinjayen Musulmi dake karkashinta, matakin da ake ganin zai sa su arangama da mutanen Yankin wadanda ke cikin ukubar rashin walwala yanzu haka.
Rikici ya so barkewa a yankin na Kashmir ne, bayan da Indiya ta soke kwarya-kwaryar ‘yancin da yankin na Kashmir dake karkashin ta ke da shi, bisa zargin cewa Pakistan kan amfani da yankin wajen kaddamar da ayyukan ta’addanci a Indiya.