Amurka ta ce ta yi amannar cewa Koriya ta Arewa tana shirin gwajin makamin nukilya a cikin wannan watan na Mayu da muke ciki, karo na farko tun bayan shekarar 2017, tana mai sabanta tayin tattaunawa don warware tankiyar da ke tsakaninsu
Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fito da wannan sanarwar ne a daidai lokacin da hankalin ta ke ci gaba da tashi a game da Koriya ta Arewar, wadda ta gudanar da gwajin makamai har 14 tun daga watan Janairu zuwa yanzu.
Nan gaba a cikin wannan watan, shugaban Amurka Joe Biden zai yi tattaki zuwa Japan da Koriya ta Kudu, inda ake sa ran batun Koriya ta Arewa zai kasance a sahun gaba a cikin abubuwan da za su tattauna.
A wani labarin na daban Gwajin da Koriya ta Arewar za ta yi na iya zuwa daidai lokacin ziyarar shugaba Biden, ko kuma ranar 10 ga watan Mayu, lokacin rantsar da zababben shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol, wanda ya sha alwashin daukar tsatsaurar matsaya a kan Koriya ta Arewa.
Amurka ta ce akwai alamun da ke nuna cewar kasar Korea ta Arewa ta mallaki tarin makaman da ba’a san adadin su ba, bayan gwajin wani makami mai linzami mafi girma da Koriyar ke cewa na iya kai wa kasar Amurka.
Mai bai wa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan ya shaidawa manema labarai cewar matakin na Korea wani yunkuri ne na takala, kuma suna tunanin cewar kasar na da tarin makaman da ba su sani ba.
Gwajin da Korea ta gudanar ranar alhamis shi ne irin sa na farko da kasar ta yi a karkashin jagorancin shugaba Kim Jong Un tun daga shekarar 2017.
Kamfanin dillancin labaran Korea ya ruwaito cewar a karkashin sanya idon shugaba Kim aka gwada shu’umin makamin wanda ya ke tabbatar da aniyar kasar na fuskantar duk wata kasa da za ta kalubalance su.
Rahotanni sun ce sabon makamin ya yi tafiyar da ya zarce duk wasu makamai masu linzamin da aka gwada a shekarun baya tare da wani da aka kera na musamman domin kai hari ko ina a cikin Amurka.