Koriya Ta Arewa Ta Yi Gwajin Makamai Masu Linzami.
Koriya ta Arewa ta yi gwajin wasu makamai masu linzami guda biyu a safiyar yau Laraba.
Ma’aikatar tsaron makobciyar kasar wato Koriya ta kudu ta ce da sanyin safiyar yau ta gano gwajin na makwabciyarta inda ta harba makaman daga Onchon da ke gab da iyakarta ta ruwa daga yammaci.
Tun watan Janairun shekarar nan rabon da Koriya ta Arewa ta yi gwajin nau’in makamin wanda baya sahun makaman da aka haramta mata gwadawa karkashin takunkuman Majalisar Dinkin Duniya.
READ MORE : Eric Trump; Muna da faifan binciken da jami’an FBI suka yi a gidan Mare Lago.
Koreya ta Arewa ta ci karo da sabbin takunkuman ne bayan manyan gwaje-gwajen da ta yi a shekarar nan cikinsu har da makami mai linzami da ke iya cin dogon zangon nahiya zuwa nahiya da rabon kasar ta harba shi tun shekarar 2017.
READ MORE : EU Ta Fara Nazarin Ra’ayin Iran Dangane Da Farfado Yarjeniyar JCPOA.
READ MORE : Kasar Kuwait Ta Nada Sabon Jakadanta Na Farko A Kasar Iran Bayan Shekaru Shida.
READ MORE : MDD Da Rasha Sun Tattauna Game Da Cibiyar Nukiliyar Zaporijjia.
READ MORE : Kenya; Wasu Mambobin Hukumar Zabe Sun Ce An Yi Magudi.