Kenya; Odinga, Ya Garzaya Kotu Domin Kalubalantar Sakamakon Zabe.
Shugaban ’yan adawa, a zaben shugabancin kasar Kenya, da aka sanar da sakamakon sa a ranar Litinin Raila Odinga ya musanta shan kaye, tare da shan alwashin garzayawa kotu, domin kalubalantar sakamakon da hukumar zaben kasar ta fitar, wanda ya ayyana mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin wanda ya yi nasara.
Odinga mai shekaru 77 da haihuwa, ya yi takarar shugabancin kasar Kenya ne a karo na 5, karkashin jam’iyyar One Kenya Coalition. Ya kuma shaidawa dandazon magoya bayansa cewa, ko alama bai gamsu da sakamakon zaben da aka bayyana ba.
Ya ce hukumar zaben kasar IEBC, ta sabawa kundin mulkin Kenya, inda ta ayyana Mr. Ruto a matsayin wanda ya lashe zaben, don haka a cewarsa, zai garzaya kotu domin bin bahasi.
READ MORE : Nijar Ta Haramta Zangar zangar Kin Jinin Sojojin Faransa Da Tsadar Rayuwa.
Hukumar zaben kasar Kenya dai ta ce Mr. Ruto ya yi nasarar lashe zaben na ranar 7 ga wata da kashi 50.49 bisa dari na jimillar kuri’un da aka kada, yayin da Raila Odinga ya samu 48.8 cikin dari.
READ MORE : Koriya Ta Arewa Ta Yi Gwajin Makamai Masu Linzami.
READ MORE : Eric Trump; Muna da faifan binciken da jami’an FBI suka yi a gidan Mare Lago.