A wannan ranakun ne shugaban Amurka Joe Biden ke ziyarar aiki a nahiyar asiya da kuma Saudiyya a karo na farko tun bayan darewar sa kujerar mulki, amma an jiyo shugaban yana tuhumar saudiyya dangane da kisan tsohon dan jaridar nan kashshogi.
Shugaba joe biden wanda ya fita ta gabar tekun jodan a matsayin wani salo na taimakawa haramtacciyar kasar Israila ya isa Saudiyya inda aka hango shi yana gaisawa da Sarkin Saudiyyan kafin daga bisani yayi zaman gani da waziri mai jiran gado Muhammad Bn Salman.
Kisan dan jarida Kashshogi da gwamnatin saudiyya tayi na cikin batutuwan da ake sa ran shugaba joe biden zaiyi amfani dasu domin tursasa masarautar saudiyya ta aiwatar da gabadayan muradan sa a wannan lokaci.
Kafar sadarwa ta BBC mallakin birtaniya ta rawaito cewa a yayin zaman gani da akayi tsakanin joe biden da Muhamman Bn Salma din biden ya tado da batun kisan kashshogi inda ya tuhumi bn salman din da kisan dan jaridan amma ba cikin gaggawa bn salman din ya musanta wannan zargi.
BBC ta rawaito cewa bn salman ya musanta wannan zargi inda ya bayyana cewa bashi da hanni ko kadan a cikin wannan batu.
Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Amurkan ke godon saudiyyan ta saki danyen man fetur da yawa a kasuwa domin amurkan ta samu saukin farashin man fetur wanda yayi tashin gwauron zabi sakamakon yakin da ake fafatawa tsakanin Rasha d Ukraine.
Masu lura da lamurran siyasa dai na ganin wannan karon afili amurkan na son amfani da batun kashshogi domin tursasa masarautar saudiyya ta biya mata bukatun ta kuma idan hakan ta faru masarautar ta saudiyya bata da wani zabi iallah ta aiwatar da abinda amurkan ta bukata.
Dan jarida kashshogi dai ya gamu da ajalin sa ne a hannun saudiyyawan bayan da ya ziyarci ofishin jakadancin saudiyyan dake turkiyya.
Kafin nan dan jaridan yana aiki da wani babban kamfanin dillacin labarai a New York.