‘Yan bindiga da ake zargin ‘yn awaren Biafra ne sun kashe ‘yan sanda 4 a mabanbantan hare-hare da suka kai a kudu maso gabashin Najeriya.
Ya ce ‘yan sanda sun yi fito na fito da su ‘yan bindigar da ake zargi ‘yan kungiyaar IPOB ne, lamarin da ya sa suka tsere zuwa wani otel don neman mafaka, amma jami’an suka bi bayansu, inda suka kame 17 daga cikinsu.
Hari na biyu
Zalika, hari na biyun da ya auku a ranar Lahadi, wani kwantan bauna ne da ‘yan bindigar suka yi a jihar Anambra, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda 2 daga cikin ayarin wani babban jammi’in gwamnatin jihar.
Samun karuwar hare-hare
Yankijn kudu maso gabashin Najeriya yana fuskantar hauhawar tashin hankali, inda a shekarar da ta gabata, ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan awaren Biafra ne suka kashe sama da ‘yan sanda 130 kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka ruwaito.
Fiye da mutane miliyan daya ne suka mutu a yakin basasa da aka shafe watanni 30 ana yi, bayan da a shekarar 1967 wasu sojoji daga ‘yan kabilar Igbo suka ayyana ‘yantatar kasar Biafra.