Kasashen Rasha Da Ukrain Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Saida Alkama.
Gwamnatocin kasashen Rasha da kuma Ukraine sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta bude tashoshio jiragen ruwa a tekun Black sea don fidda alakama wadanda aka sayar zuwa kasashen duniya a jiya Jumma’a.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya cewa kasashen biyu suna daga cikin manya-manyan kasashen duniya wadanda suke noman kayakin abinci musamman alkama a duniya, amma yakin da suke fafatawa tun watan Fabrairun da ya gabata ya tsaida fito da abinci zuwa kasar Duniya da tashoshin jiragen ruwa na Tekun Black Sea, wanda ya kaiga alkaman da Ukrai take fitarwa yay i kasa har zuwa kasha 1\6 na abinda ta saba fitarwa kafin ta shiga yaki da Rasha.
READ MORE : Faransa; Yan Majalisar Dokoki Da Dama Sun Ya Yi Allwadai Da Tsarin Wariya Na Isra’ila A Falasdinu Da Ta.
Ministan tsaron kasar Rasha Sergei Shoigu da minister raya kasa na Ukrain, Oleksandr Kubrakov suka rattaba hannu kan yarjeniyar nesa da juna don kasa su mikawa juna hannu a wani Hotel a kasar Turkiyya. Wanda kuma shugaban kasar ta Turkiya Rajab tayyib Urdugan da babban sakatren MDD Antonio Gutess suka sanya ido a kan rattaba hannun.