Shugaban Algeria AbdelMajid Tebbourne ya haramta fitar da kayayyakin abinci zuwa kasashen ketare a daidai lokacin da ake ci gaba da fargabar tashin farashin kayayyakin abinci saboda rikicin Rasha da Ukraine, yayin da masana ke cewa, matsalar ka iya haifar da yunwa a kasashen Larabawa.
Shugaban na Algeria ya dauki matakin ne bayan ya saurari jawabin da Ma’aikatun Noma da Kwadago na kasar suka gabatar masa game da abincin da aka fi ta’ammulli da su a kasar.
A bangare guda, rahotanni na cewa, iyalai da dama a daukacin sassan yankin Arewacin Afrika na ci gaba da rige-rigen sayo nau’ukan abinci irinsu filawa da garin masara suna adana su, saboda fargabar tashin farashin abinci a dalilin yakin Rasha da Ukraine.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage ‘yan makwanni a fara gudanar da azumin watan Ramnadan, lokacin da iyalai suka fi wadata kansu da abinci.
Tunisia da Morocco da Libya da sauran kasashen Larabawa, na shigo da alkama ne daga Rasha da Ukraine da ke gwabza yaki a yanzu haka.
A wani labarin na daban Amurka ta gargadi China game da yunkurin taimaka wa Rasha a yakin da take yi da Ukraine, matukar ba haka ba kuma zata dandana kudarta.
Sai dai kuma tuni ma’aikatar harkokin wajen China ta musanta zargin, inda ta ke cewa da gangan Amurka ta bullo da wannan zancen don kawai jefa ta cikin rikicin da gangan.
Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawa ta musamman da aka yi a tsakanin ministocin kasashen wajen Amurka da China a birnin Rome.
A yanzu haka dai bayanai na cewa za a koma ci gaba da tattaunawar zaman lafiya a tsakanin kasashen Ukraine da Rasha karo na Hudu a gobe Talata.
A cewar guda daga cikin tawagar Ukraine a tattaunawa da Rasha, Mikhailo Podolyak ta cikin wata wallafar shafin Twitter, yace yana fatan a wannan karo zaa cimma matsaya.