Kasashen G7, Sun Amince Da Dakatar Da Shigo Da Mai Daga Rasha.
Shugabannin kasashen G7 mafiya karfin tattalin arziki a duniya, sun sun amince da hanawa ko kuma dakatar da shigo da mai na Rasha.
Bangarorin sun bayyana hakan ne yayin taron da suka gudanar da kafar bidiyo, bisa shawarar da shugaban Amurka Joe Biden, ya bayar in ji fadar White House.
A cikin sanarwar da suka fitar, shugabannin na G7 sun kuma yi kira ga Moscow da ta dage takunkumin hana fitar da alkama daga kasar Ukraine, wanda ke barazana ga duniya da matsalar karancin abinci.
Sun kuma lashi takobin ci gaba da kai sanya takunkumi kan manyan masu kudi na Rasha da ‘yan uwan shugaba Vladimir Putin.
READ MORE : Abdollahian; Ziyarar Assad Ta Bude Wani Sabon Shafi Na Huldar Dake Tsakanin Iran Da Siriya.
Amurka, dai tuni ta kakaba wa kasar Rasha takunkumin man fetur, yayin da kungiyar Tarayyar Turai ke ci gaba da tattaunawa kan nata, duk da cewa dai batun ya haifar da rarrabuwar kai tsakanin kasashen turan.
READ MORE : Ivory Coast Na Karbar Taron Duniya Na COP-15 Kan Kare Muhalli.
READ MORE : Ganduje Ya Zabi Mataimakin Sa Nasir Gawuna A Matsayin Wanda Zai Gaje Shi.