Najeriya; Kamfanonin Jiragen Sama Sun Janye Shiga Yajin Aiki.
Kungiyar kamfanonin sufurin jiragen sama a Najeriya ta sanar da janye shiga yajin aikin data kudiri anniyar yi a wannan Litinin.
Bayanai sun ce matakin ya biyo bayan da gwamnatin Najeriya ta baiwa kungiyar tabbacin cewa za ta shiga tsakaninsu da kamfanonin da ke samar da man fetur da jirgi ke amfani da shi.
Saidai kungiyar ta ce ta bai wa gwamnatin Najeriyar wa’adin kwana biyu don ta lalubo hanyoyin saukaka musu wajen samun man jirgi mai arha.
Dama dai kungiyar ta ce za ta shiga yajin aikin ne saboda tsadar man fetur da jirgi ke amfani da shi, ko da yake wasu rahotannin sun ce ba dukan kamfanonin sufurin jiragen ne ba suka amshi kiran kungiyar na shiga yajin aikin.
READ MORE : Kasashen G7, Sun Amince Da Dakatar Da Shigo Da Mai Daga Rasha.
Masana harkar tattalkin arziki sun bayyana cewa shiga yajin aikin kamfanonin zai iya ragargaza tattalin arikin kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika musamman a wannan lokaci da al’amuran suka tagayyara sakamakon rikicin Rasha da Ukraine.
READ MORE : Bashar Assad Shugaban Kasar Syria Na Ziyara A Tehran.
READ MORE : Hungary Ta Takawa (EU) Birki Kan Kakabawa Man Fetur Din Rasha Takunkumi.