Tarayyar Turai ta ce nazarin da ta yi a kan sunayen wadanda Taliban ta bai wa manyan makaman gwamnati ya nuna cewa kungiyar ba ta cika alkawarin da ta yin a kafa gwamnatin da ya kunshi dukkannin bangarorin.
Kasashe 27 na kungiya Tarayyar Turai sun gindaya sharruda biyar da cika su zai yaukaka dasawarsu da Taliban, ciki har da kafa gwamnatin wucin gadi da za ta wakilci ilahirin al’ummar kasar.
Tuni dai sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fara tattaunawa da wasu kasashen duniya dangane da makomar Afghanistan, inda ya gana da ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas, gabanin taron kasashen G20 a kan kasar.
Ita ko China, na’am ta yi da kawo karshen makonni 3 na tabarbarewar doka da oda a Afghanistan sakamakon kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya, tana mai kira ga Taliban ta maido da kasar cikin hayyacinta.
A ranar Talatar nan ne Taliban ta kaddamar da gwamnatin rikon kwarya wadda babu mata ko wadanda ba ‘yan kungiyar ba, kuma ta kunshi jami’anta da ke karkashin takunkuman majalisar dinkin duniya
Ita ko jamhuriyar musulunci ta Iran wacce itace makociya ta kurkusa da afghanistan din kuma itace take da kamanceceniya da suka hada na tarihi al’adu da kuma yaren farisanci wanda suke magana dashi gabadaya.
Jamhuriyar musulunci ta Iran din a ta baki jami’an gwamnatin ta ta nuna gamsuwar ta yadda aka tabbatar da an fatattaki amurka daga kasar afghanistan kuma tayi maraba da sabuwar gwamnatin bisa sharadin sabuwar gwamnatin zata mutunta bangarorin al’ummar kasar, kama daga bangarorin kabilu addinai dama akidu.