Kan Kasashen Turai Ya Rabu A Lokacinda Rasha Ta Rufe Fampon Isakar Gas Ga Wasu Kasashe.
A dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Rasha ta rufe fampon iskar gas ga kasashen Poland da Bulgeriya saboda kin sayan sa da kudaden Rasha wato roubles, tuni kamfanonin samar da iskar gas na kasashen Jamus da Italiya suka bude asusun roubles a bankunan Rasha a turai don sayan iskar gas kamar yadda shugaba Putin ya bukata.
Tashar talabijin ta Aljazeera na turanci ta bayyana cewa kan kasashen Turai a rabe yaki dangane da sayan iskar gas daga kasar Rasha da roubles a dai lokacinda shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce babu gas idan ba’a biya da roubles ba.
Kungiyar tarayyar Turai tana kokarin ganin dukkan kasashen kungiyar wadanda suka dogara da kasar Rasha don sayan iskar gas su hada kai don tunkurar kasar Rasha kan yakin da take a Ukrain sannan su sami wasu hanyoyi na samun iskar gas ko makamashi ba daga kasar Rash aba. Amma da alamun kungiyar ta kasa hadin kan kasashen kan kan hakan.
A halin yanzu dai da alamun kasar rasha ta sami naara a kansu, don a dole zasu saye iskar gasa da sauran bukatunsu na makamashi daga kasar Rasha da kuma kudadenta, alhali su suka fara dora mata takunkuman tattalin arziki.
Labarin ya kammala da cewa Rasha zata sami kimani dallar Amurka miliyon $850 a ko wace rana daga kasashen na Turai, wanda zaio bada damar ci gaba da yaki a kasar ta Ukrain.