Kamaru ta zama kasa ta farko da ta samu tikitin zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin Afrika da take karbar bakunci, bayan da ta lallasa Habasha da 4-1 a Yaounde.
A halin yanzu, tazarar maki uku Kamaru ta baiwa Burkina Faso da Cape Verde, wadanda suka kara a daren ranar Alhamis a Yaounde, ‘yan wasan Burkina Faso suka yi nasara da ci 1-0, sakamakon kwallon da Hassane Bande, na Ajax ya ci a farkon wasan.
A bangaren Habasha dai har yanzu tana neman maki na farko da kuma nasarar farko wadanda rabon ta same su tun gasar cin kofin kasashen Afirka ta shekarar 1976.
Rabon da Habasha ta lashe gasar AFCON dai tun a shekarar 1962.
A wani labarin na daban Bayan shafe kwanaki ana cece-kuce akan Janny Sikazwe, alkalin wasa dan kasar da ya jagoranci wasan da aka buga tsakanin Tunisia da Mali a ranar Laraba, an gano dalilinsa na busa usur din kawo karshen fafatawar kafin lokaci ya cika har sau biyu.
Sai dai a yayin da yake karin bayani akan lamarin, shugaban alkalan wasan da ke alkalanci a wasannin gasar cin kofin Afirka, Essam Abdel-Fatah, ya ce alkali Janny Sikazwe yayi fama ne da matsalar tsananin zafin da makinsa ya kai 34 a ma’aunin Celcius abinda ya haifar da karancin ruwa a jikinsa.
Abdel-Fatah ya kara da cewar ko bayan Karkare wasan da Mali ta doke Tunisia da 1-0 a filin was ana Limbe da ke Kamaru, sai da aka gaggauta garzawaya da Alkali Sikazwe asibiti domin ceto lafiyarsa.