Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta zargi gwamnatin Kamaru da na Amurka da aikata “take hakkin dan adam” mafi muni kan ‘yan kasar da dama da Amurka ta mayar da su kasar da ke yankin tsakiyar Afirka.
Inda suka fuskanci tsarewa ba bisa ka’ida ba; bacewar wasu; azabtarwa da fyade, da kuma sauran tashin hankali, ko kuma karban cin hanci.
Yankin ‘Yan aware
Kusan dukkanin wadanda Amurkan ta dawo da su gida Kamaru, sun fito ne daga yankin tsirarun masu amfani da turancin Ingilishi a yammacin kasar, inda mayakan ‘yan awaren dake neman ballewa domin kafa kasar Ambazonia ke fafatawa da sojojin gwamnati da suka shafe shekaru biyar cikin kazamin rikici, inda Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi masu zaman kansu ke zargin bangarorin biyu da cin zarafin jama’a.
Rahotan yace “da yawa daga cikin mutanen sun fuskanci cin zarafi da suka hada da amfani da karfi fiye da kima, rashin kulawar likita, da sauran cin zarafi a hannun hukumomin Shige da Fice da Hukumar Kwastam na Amurka.
Amurka ta keta ‘yancin mafaka
Kungiyar tace da wannan mataki da Amurka ta dauko na maido da ‘yan kasar Kamaru gida duk da ta kwana da sanin barazanar zalunci da suke fuskantar da azabtarwa, to lallai ta keta ‘yan mafaka da na kare hakkin bil’adama.”
Gwmanatin Trump
Rahoton ya ce an kori mutanen ne a karkashin gwamnatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, “wanda ke da tsattsauran ra’ayi na shige da fice, da takaita samun mafaka, da kalaman wariyar launin fata,”
Gwamantin Biden
HRW tace, yayin da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta “dauki kyakkyawar matakin soke wani jirgin ‘yan kasar Kamaru zuwa gida a watan Fabrairun shekarar 2021, amma abin takaici ta kori ‘yan kasar da dama cikin watan Oktoba.