Na’urar bibiya ta tsaro ta nuna yadda matsalar ta shafi mutane da dama da ke amfani da Kafafen sada zumuntar, musamman a birnin Washington na Amurka da kuma Paris na kasar Faransa.
Mai Magana da yawun kamfanin Facebook daya daga cikin Kafafen yada labaran, Andy Stone a shafinsa na Twitter ya wallafa cewa, suna sane da matsalar da ta kunno kai ta gaza shiga manhajojin kan wayar salula, amma suna kokarin shawo kan matsalar nan bada jimawa ba.
Wannan katsewar na zuwa ne kwana guda bayan wata mai tseguntawa ta ziyarci wani gidan talabijin na Amurka don bayyana yadda ta bankado wasu takardu ga hukumomi da ke zargin kamfanin Facebook da rura matsalar nuna tsana da kuma gurbata lafiyar kwakwalwar kanana yara.
A wani labarin na daban sakamakon fitar da wasu mahimman takardu da ke bayyana yadda dimbim fitattun mutane a duniya suka boye tarin dukiyoyi da suka kai miliyoyin Dala a asusun ajiyar kasashen ketare da babu haraji, gwamnatoci sun yunkuro don rage tasirin wannan tonon sililin na binciken da aka yi wa lakabi da ‘Pandora Papers’
Sunayen wasu shugabannin 35, tsaffi da masu ci ne suka bayyana a wasu kundaye da suka kai akalla miliyan 11 da dubu 900 da aka bankado daga cibiyoyin kudi a fadin duniya wanda aka yi wa lakabi da ‘Pandora Papers’.
Cikin wadanda sunayensu suka bayyana a wandannan kundaye ,akwai tsohon Fiiraministan Birtaniya, wanda aka nuna ya kauce wa biyan harajin kan wani gidansa na birnin Landan.
Babu sunan shugaban Rasha Vladimir Putin, amma kuma an danganta shi da wasu kadarori na makusantansa a birnin Monaco na Faransa, musamman wani gida na kusa da teku, mallakin wata mata da suka haihu da ita.
Sai dai kakakin fadar Kremlin ta Rasha, Dmitry Peskov ya ce, zargi ne mara tushi.
Ita ma Jordan ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin watsi da rahoton cewa ,an bankado tarin kadarori da suka kai miliyan 100 na Dala da Sarki Abdallah na biyu ya tara a California da Landan.
Cibiyar ‘yan jarida ta kasa da kasa ta gudanar da wannan bincike, wanda kafofin yada labarai da suka hada da Washington Post, BBC da Guardian suka watsa