Bankin Duniya na shirin kafa asusun gaggawa na Dala biliyann 170 domin taimaka wa kasashe matalauta da ke fama da tarin matsaloli.
Malpass ya ce, tarin basuka da kuma tashin farashin kayayaki na a matsayin manyan matsaloli guda biyu da ke barazana ga habbakar tatttalin arzikin duniya.
Shugaban Bankin Duniyar ya ce, yana cikin damuwa kan halin da kasashe masu tasowa ke ciki, inda suke fuskantar tsadar farashin makamashi da taki da kuma abinci.
A makon jiya ne, Bankin Duniyar mai cibiya a birnin Washington ya rage hasashensa na habbakar tattalin arzikin duniya a bana, yayin da shi ma asusun Lamuni na IMF ake sa ran zai rage nasa hasashen a wannan Talatar.
Malpass ya ce, asusun gaggawar na tsawon watanni 15, zai ci gaba da wanzuwa har zuwa Yunin shekarar 2023, inda kuma zai maye gurbin asusun rage radadin tasirin annobar Covid-19 da zai kawo karshe a watan Yunin bana.