Fitaccen dan damben boxing ajin masu nauyi Anthony Joshua dan Ingila, ya yi watsi da rahotannin cewa ya amince da yarjejeniyar karbar fam miliyan 15 kwatankwacin Yuro miliyan 18 don janyewa daga shirin sake karawa da Oleksandr Usyk na kasar Ukraine.
A watan Satumban shekarar bara ne dai Usyk ya kwace dukkanin kambun Joshua na WBA da IBF da kuma WBO, bayan lallasa Joshuan da yayi a fafatawar da suka yi.
Rashin nasarar da Joshua ya yi a karon battarsa da Oleksandr Usyk, itace karo na biyu da fitaccen dan damben boxing din ya fuskanta tun bayan ficen da yayi.
A baya bayan nan ne kuma kafafen yada labarai da dama ciki har da na kasar Birtaniya suka wallafa rahoton cewa, Joshua ya yarda Usyk ya biya fam miliyan 15, domin janyewa da shirin sake fafatawar da aka tsar za su yi, labarin da fitaccen dan damben dan asalin Najeriya ya bayyana a matsayin mara tushe.
A karshen watan Satumban da ya gabata, fitaccen dan damben boxing na Ingila ya kafe kan cewa zai iya fafatawa da Tyson Fury wani fitaccen dan damben na boxing wani lokaci nan gaba kadan, koda kuwa ba tare da kambunansa guda uku na duniya ba.
A wani labarin na daban wata kotu a Senegal ta yanke hukuncin daurin rai da rai akan shugaban Yan Tawayen Casamance Cesar Atoute Badiate saboda samun sa da laifin kisa bayan ya kaddamar da boren da yayi sanadiyar mutuwar mutane 14.
Lauyan sa Cire Cledor ya kuma ce bayan Cesar an kuma daure wasu mutane biyu da suka hada da Omar Ampoi Bodian da dam jarida Rene Capain Bassene rai da rai a kotun dake Ziguinchor.
A cikin watan Maris na shekarar 2022,Rundunar sojin kasar Senegal ta kaddamar da farmaki kan mayakan da ke kawance da mayakan ‘yan tawayen ‘Casamance’, wata kungiyar ‘yan aware a yankin kudancin kasar.
A ranar 13 ga watan na Maris, sojojin kasar na Senegal suka kaddamar da farmakin kan mayakan ‘yan awaren na Casamance da ake kira da MFDC a takaice, wadanda suke karkashin jagorancin Salif Sadio.
Tun a shekarar 1982 mayakan ‘yan awaren na Senegal suka fara fafutukar yaki da gwamnatin Senegal, bisa zargin gwamnatin kasar da mayar da su saniyar ware.
Mutane 16 ne aka tuhuma da laifin kashe mutane 14 da suka je daji omin neman itace a Bayotte dake kusa da Ziguinchor ranar 6 g awatan Janairun shekarar 2018.