Rahotanni daga kasar amurka na tabbatar da cewa shugaba joe biden na amurkan ya shirya tsaf domin kai ziyarar aiki gabasa ta tsakiya inda ake sa ran zai ziyarci kasar saudiyya a karo na farko.
Amma sai dai masana suna ganin ya zuwa yanzu shugaba joe biden din bashi da tsayayyiyar ajanda domin tunkarar ‘yan gidan sarautar saudiyyan amma dai ana sa ran daga cikin manyan batutuwan da zasu kai shugaban na amurka saudiyya a kwai batun tashin farashin man fetur sakamakon yakin Rusga da Ukraine sai kuma batun samawa haramtacciyar kasar isra’ila gindin zama.
Isra’ila dai a ‘yan watannin nan na fuskantar matsalolin da bata taba fuskantar irin su ba a tarihin kafuwar ta.
Duk da kokarin amurka lokacin tsohon shugaba Trump na shirin karni tsakanin shugabannin kasashen larabawa da haramtaciiyar kasar isra’ilan, amma dai alamu suna nuna har yanzu isra’ila tana cikin gagarumar matsala kuma tana ma shirin rugujewa.
Masana dai suna ganin duk da matsalar da isra’ilan take ciki amma batun tashin farashin man fetur sakamakon yakin Rasha Da Ukraine shine zai zama abu mafi muhimmanci da shugaba joe biden din zai sa a gaba a ziyarar tasa a gabas ta tsakiya.
Duk da dai masu magana da yawun gwamnatin Amurkan sun musanta cewa shugaban zaije saudiyya ne domin matsalar tashin farashin makamashin inda suka bige ta cewa, shugaban zaije saudiyyan ne domin batutuwa da suka shafi shirya isra’ilan da kasashen larabawa da kuma akwo karshen yakin saudiyyan da kasar yemen.
Wasu daga cikin batutuwan da masu magana da ywun fadar gwamnatin amurkan sukayi da’awar zasu kai shugaban na Amurka saudiyyan sune, samo hanyar da za’a maganta barazanar Jamhuriyar Musulunci Ta Iran, shawo kan matsalar dumamar yanayi dakuma yaki da ta’addanci.
Masana sun tabbatar da cewa wannan yana nuna kasa a gwuiwan shugaba biden din a lamarin gabasa ta tsakiya duba da gagarumin kayen da amurkan se sha a hannun Iran a watannin da suka gabata.