Shafin yada labarai na Mawazin ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar cibiyar ilimi ta jami’ar Azhar ta sanar da cikakken goyon bayanta ga gwamnatin kasar iraki wajen yaki da ta’adanci a fadin kasar.
Bayanin na jami’ar Azhar ya ce, masu kaddamar da hare-haren ta’addanci da sunan addini, abin da suke yi ba shi da wata alaka da addinin mulsunci, kamar yadda kuma ya yi hannun riga da ‘yan adamtaka, a kan haka gwamnatin Iraki hakki ne a kanta ta yaki wadannan masharranta.
Haka nan kuma jami’ar Azhar ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren ta’addancin da aka kai kan lardin Salahuddin a ranar Asabar da ta gabata, inda jami’an tsaro da fararen hula suka rasa rayukansu, hare-haren da ‘yan ta’addan takfir na Daesh suka dauki nauyin kaddamar ad su.
A cikin kwanakin nan dai kungiyar daesh ta fara dawowa da hare-harenta na ta’addanci a kasar Iraki, wanda kuma hakan yana zuwa ne a daidai lokacin da al’ummar Iraki suke matsa lamba kan Aurka da ta fitar ad sojojinta daga kasar, yayin da kuma wasu bayanai na tsaro daga bangarori daban-daban a kasar ta Iraki suke yin ishara da cewa, Amurka tana da kyakkyawar alaka da kungiyar ta Daesh a cikin kasar ta Iraki.
Kasar ta iaraki dai na fama da matsalolin tsaro wadand suka hada da kungiyoyin tada kayar baya masu tsatstsauran ra’ayin wahabiyanci.
Tuni dai majalisar kasar ta yanke hukuncin korar sojojin amurka daga kasar domina cewar ‘yan majalisun, hadakar sojojin amurkan na bada gagarumar gudummmawa wajen samar da rashin tsaro a fadin kasar ta Iraki.
Kasar Iraki wacce ke makotaka da jamhuriyyar musulunci ta Iran kuma take da rinjayen mabiya mazhabar shi’anci dai ta zabi yadda da makociyar ta Iran din bisa amurka wacce ake ganin ta kawo nakasu a bangaren tsaron kasar tun bayan shigar ta kasar.