Jami’an diflomasiyyar Faransa za su shiga yajin aiki a wata mai zuwa, karo na biyu a tarihin kasar, a wani yunkuri na nuna rashin amincewarsu da sauye-sauyen gwamnati da kungiyoyin kwadagon suka ce zai kawo cikas ga ma’aikatar harkokin wajen kasar a dai dai lokacin da duniya ke cikin halin tsaka mai wuya.
Jami’an kungiyoyin suka ce wadannan matakai na rusa aiyukan diflomasiyya bazaiyi tasiri ba, a dai dai lokacin da yake yake suka mamayi Yankin Turai, cikin wani sakon hadin gwiwa da kungiyoyin suka fitar.
Cikin sauye-sauyen da Shugaba Emmanuel Macron ya gabatar aka yi gaggawar aiwatar wa, bisa doka a watan Afrilu, manyan jami’an ma’aikatar harkokin waje za su rasa matsayinsu na musamman kuma za’a tsunduma su cikin jiga jigan ma’aikatan gwamnati shafaffu da mai.
Yin hakan na nufin za’a tura manyan jami’an Diflomasiya a kalla 700 wasu ma’aikatu da basu shafi bangaren diflomasiya ba don cigaba da gudanar da aiyukan su.
Yayin da wani jami’in diflomasiyar da ya yi magana ba tare da baiyana sunan sa ba ya baiyana cewar sun kasance cikin matukar damuwa domin ba’a sauya matsayin su na aiki amma yana daraja abokan aikin sa na sassan a kasar domin bai san yadda zai gudanar da irin aiyukan su ba suma kuma basu san nasa ba.
Faransa ce dai kasa ta uku mafi girma a harkokin kasashen ketare a duniya bayan China da Amurka, tare da ma’aikata kusan 14,000 a ma’aikatar harkokin waje gaba dayan ta.
Wannan yajin aikin dai za a fara shi ne a ranar 2 ga yunin wannan shekarar ta 2022.