‘Yan majalisar dokokin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun kada kuri’ar amincewa da soke hukuncin kisa, matakin da suka aiwatar a ranar Juma’ar da ta gabata.
Kasar dai ta bi sahun Chadi a shekarar 2020 da Saliyo a shekarar bara wajen kawo karshen hukuncin kisa a nahiyar Afirka a shekarun baya bayan nan.
Hukuncin kisa na karshe da aka zartas a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya ya kasance a shekarar 1981.
A wani labarin na daban kuma tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta ce ta fara gudanar da bincike kan rahotannin kashe fararen hula da dama da ake zargin sojojin kasar da kuma sojojin hayar wani kamfanin tsaron Rasha da aikatawa.
A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu, sojoji da abokan kawancen su, sun kai hari a kauyukan Gordil da Ndah, da ke arewa maso gabashin birnin Bangui, wanda ya yi sanadiyar kashe fararen hula.
Babbar jami’ar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin bil’adama, Michelle Bachelet, ta yi Allah wadai da take hakkin bil’adama da aka yi a kasar, da suka hada da kashe ‘yan ba ruwan mu da cin zarafin mata, da kungiyoyin ‘yan tawaye da kuma sojojin kasar da kawayensu na Rasha ke aikatawa.