Kafin haka dai Alkalin alkalan kasar Iran Gholam-Hossein Mohseni-Ejei ya rubutawa Imam Khamenei wasika inda a cikinta, ya bukaci jagoran ya yi rangwame ko ya yafewa fursunoni 2,825 hukuncin da aka yanken masu a kutuna daban-daban na kasar saboda zagayowar wadannan kwanaki farin ciki masu alfarma.
A wani labarin na daban kuma daga nahiyar afirka kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani sako da shugaban kungiyar Hamas Isma’il Haniyya ya aike wa babban kwamishinan kungiyar tarayyar Afirka Musa Faki Muhammad, ya bayyana matukar damuwa kan wannan mataki da kungiyar ta dauka.
Haniyya ya bayyana cewa, wannan mataki ya saba wa abin da aka san siyasar kungiyar Tarayyar Afirka a kansa, na nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Falastinu da kuam fafutuka wajen kare hakkokinsu, domin kuwa bai wa Isra’ila wannan kujera a cikin kungiyar tarayyar Afirka, hakan yana a matsayin amincewa da dukkanin auukan da take aikatawa na kisan kiyashi akan al’ummar Falastinu.
A kan haka Haniyya, ya bukaci babban kwamishinan na kungiyar Tarayyar Afirka, da a sake yin nazari kan wannan mataki tare da janye shi, domin tabbatar da cewa tarayyar Afirka tana nan kan bakanta na kare wadanda ake zalunta, da kuma kin jinin duk wani nau’in mulki na zalunci da wariya akan wasu al’umma.
Ita ma a nata bangaren gwamnatin kasar Namibia ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta nisanta kanta daga matakin da kungiyar Tarayyar Afirka ta daukana baiwa Isra’ila kujera a cikin kungiyar, inda gwamnatin Namibia ta ce wannan ya hannun riga da tabbatattun ka’idoji na kungiyar, kuma tana yin Allawadai da hakan.
Kafin wannan lokacin ma kasashen Afirka ta kudu da Aljeriya sun fitar da bayanai da ke nuna rashin amincewarsu da wannan mataki, tare da bayyana cewa ba tare da amincewar dukkanin kasashen Afirka ne ba kungiyar ta yanke wannan shawara.