A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan idin aikon Manzon Rahama Khatamil Anbiya’a, Muhammad Mustafa (a.s), Jagora Ayatullah Khamenei, jagoran juyin juya halin Musulunci, a wata ganawa da jami’ai da wakilai na tsarin mulki, jakadu da wakilan kasashen musulmi da kuma wasu gungun mutane daga sassa daban-daban na al’ummar Iran, ya ce amsa kiran aiken annabci it ace sanadin bunkasa da jindadin duniya da lahira.
Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) na -ABNA- ya bayar da rahoton cewa, A daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan idin aikon Manzon Rahama Khatamil Anbiya’a, Muhammad Mustafa (a.s), Jagora Ayatullah Khamenei, jagoran juyin juya halin Musulunci, a wata ganawa da jami’ai da wakilai na tsarin mulki, jakadu da wakilan kasashen musulmi da kuma wasu gungun mutane daga sassa daban-daban na al’ummar Iran, ya ce amsa kiran aiken annabci it ace sanadin bunkasa da jindadin duniya da lahira. tare da ishara da mummunan abin da ya faru a zirin Gaza da kuma ci gaba da aikta laifuffukan da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke yi, Jagora ya ce: Musibar Gaza musiba ce ta bil’adama, kuma hakan yana nuna cewa tsarin duniya na yanzu ba shi da inganci kuma ba shi da damar dorewa kuma zai wargaje.
A cikin wannan taro dai Jagoran juyin juya halin Musulunci ya taya al’ummar Iran da daukacin al’ummar musulmi murnar zagayowar ranar Idin Mab’ath – ranar da aka aiko Annabi Muhmmad SAWA a matsayin manzo ga dukkan halitta-, tare da bayyana ta a matsayin mafi falala kuma mafi girma a tarihin bil’adama yana mai cewa: Da zuwan Annabi mai girma, an gabatar da cikakken makura na dindindin na jin daɗin duniya da na lahira.
Ya dauki hudowar da bunlowar sakon Annabta a cikin wani yanayi mai duhu mai cike da karkata da kauce hanya da karkatar jahiliyya tare da bayyanar da alamomin karkacewa da ci baya a cikin dukkanin manyan wayewar wannan lokaci a duniya a matsayin wani lamari na ban mamaki sannan ya kara da cewa: manufar tsarin aike shine bude hanyar sadarwa ta dan Adam da ke kunshe cikin kuntatar tsarin abin duniya tare da duniyar gaibi da Ubangijintaka, wato yin imani sannan kuma tsarkake mutum yana nufin daukaka shi da girma ta hanyar kawar da aibi da kawar da kyama, sharri da bata.
Jagora na juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kira tsarkakewa a matsayin wani gagarumin yunkuri na gyara al’amuran mutum da al’umma daga dukkanin bangarori na siyasa da tattalin arziki da zamantakewa da kawar da duk wani nau’i na zalunci da gibin akida yana mai cewa: tsarkakewa yana samar da tushen tarbiyyar mutum da al’umma ta hanyar wadatar da al’umma ta fuskar ilimi, da ruhi tare kuma da gina mutum daidai da Musulunci.
Bisa dogaro da ayoyin Alkur’ani mai girma, ya dauki aike da kiran Manzon Allah a matsayin wani abu mai gudana na yau da kullum kuma madawwami, inda ya ce: Har yanzu Manzon Allah (S.A.W) yana kan karantarwa da tsarkakewa, wato; kamar yadda ya kira mutane da su nisanci gumaka a wacen lokacin, yau ma akwai wannan zancen da kiran.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya kira yaki fito na fito mujahada da son zuciya da karya gumakan son zuciya a matsayin matakin farko na amsa kiran manzon Allah sallal Lahu alayhi wa alihi wa sallam ya kuma kara da cewa: Wasu mutane suna cewa domin gyara duniya sai ka fara gyara kanka da al’ummar ka, maganar gaskiya ce domin ta nuna gabatar da misali da aka gyara ga duniya zai jawo hankalin wasu zuwa ga wannan misali ya zamo abin koyi.
Malamin ya kira tabbatar juyin juya halin Musulunci sakamakon yadda mutane suka amsa ga sakon manzo SAWA da kuma kiran Imam mai girma inda ya ce: Al’ummarmu sun ci gaba da tafiya ta hanya madaidaiciya tare da samun nasara da yardar Allah, kuma matukar ana ci gaba da amsa kiran Annabi, bunkasa da ci gaba, wanda ba wai kawai ci gaban ruhi da lahira ba, yana mai ci gabantar da mutum ta hanyar da zai iya samun mafi kyawun misali na rayuwar duniya da lahira.
Ayatullah Khamenei kuma yayin da yake ishara da yadda zalunci da rashin adalci suka yawaita a duniya a yau, ya ce kawar da wannan yanayi da kyautata rayuwar al’ummar duniya ya dogara ne da amsa kiran manzon Allah da amfani da tsarkakuwa da karantarwar manzon Allah da karantar da su. Ya kara da cewa: alhakin da ya rataya a wuyanmu shi ne inganta kanmu da kuma nuna gudanar da mulkin kasar bisa ga abin koyi na Musulunci wanda mun samu nasarori a wannan fanni da suke da tasiri a duniya, amma duk da ba shakka muna da nakasu.
A wani bangare na jawabin nasa, Jagora juyin juya halin Musulunci, yayin da yake ishara da ci gaba da wannan musiba a Gaza, ya bayyana hakan a matsayin musibar duniyar musulmi, kai tama dukkanin bil’adama, kuma hakan na nuni da kololuwar lalacewar tsarin duniya a halin yanzu.
Ya kara da cewa: A yau, Amurka, Ingila da kasashen Turai da dama da mabiyansu suna goyon bayan Hannun masu laifi da zubar da jini na gwamnatin Sahayoniya suna nan, inda za mu iya fahimtar cewa tsarin duniya na yanzu lalataccen tsari ne kuma ba zi yiwu ya dore ba kuma zai wargaje.
Ya dauki harin ruwan bam-bamai da haramtacciyr kasar Isra’ila ta kai kan asibitoci da masallatai da gidaje tare da kashe kusan mutane 30,000 a Gaza a matsayin abin kunya ga al’adu da wayewar kasashen yamma sannan ya kara da cewa: A bayan wadannan laifuka akwai taimakon kudi da makamai da taimakon siyasa na Amurka, kuma kamar yadda yahudawan sahyoniya da kansu suka ikrarin cewa ba za su da ikon ci gaba da yakin ba tare da taimakon makaman Amurka ba, don haka Amurkawa suna da laifi kuma suna da alhakin wannan mummunan lamari.
Jagora Ayatullah Khamenei ya kira janyewar manyan kasashen yammacin duniya daga wannan lamari a matsayin mafita ga kawo karshen rikicin na Gaza yana mai cewa: ‘yan gwagwarmayar Palastinawa suna da karfin tafiyar da fagen, wanda kuma bugu da kari har zuwa yau ta fuskancin gudanar da fagen ba’a kai masu wani hari mai illatarwa ba.
Jagora yayin da yake jaddada cewa aikin da yah au kan gwamnatoci shi ne yanke tallafin siyasa, sadarwa, da makamai, da kuma rashin aika kayayyakin masarufi zuwa ga gwamnatin sahyoniyawa, ya yi nuni da cewa, ya zama wajibi al’ummu su matsa lamba kan gwamnatocinsu wajen aiwatar da wannan gagarumin aiki.
A farkon wannan taro, shugaba Hujjatul-Islam Wal-Muslimin Raisi, a jawabinsa na cewa Munasabar Maba’ath ita ce mafi girman bayyanar falalar Ubangiji, ma’ana ni’imar shiriya, ya lissafta kiran da Manzon Allah (SAW) ya yi. (S.A.W) zuwa ga tauhidi tare da kira zuwa ga tuntuni da adalci da kuma darajojin Ubangiji, yana mai ishara da kamanceceniya da kwanaki goma na Alfirijin juyin juya halin Musulunci da Idin Maba’ath, inda ya ce: amsa kiran Imam Khumaini na bauta wa Allah Madaukakin Sarki ne da yaki da talauci fasadi da wariya, ta fuskacin al’ummar Iran wata alama ce ta amsa sakon aiken annabci.
Shugaban ya kuma yi la’akari da kisan kiyashi da kisan gilla da ake yi a Gaza a matsayin abin da ke haifar da share duk wani nau’i na dukkanin ikirarin kare hakkin bil’adama na kasashen yammacin duniya, kuma wata alama ce karara ta gazawar kungiyoyin kasa da kasa ya kuma kara da cewa: Muna da tabbacin cewa jinin shahidan Gazan da Palastinu zai kawo karshen gwamnatin sahyoniyawa da kuma tsarin rashin adalci da ake ciki a yanzu.
Malam Sayyid Raisi ya karanta manufofin cikin gida da tsare-tsare na gwamnati a cikin hanyar fadada adalci, cike gurbin koma baya da kuma inganta yanayin tattalin arziki sannan ya jaddada cewa: mafita daya tilo da za a magance matsalolin ita ce dogaro da ikon cikin gida, kuma gwamnati ba ta dogaro da hannun ‘yan kasashen waje domin magance matsalolin kasar.
Source: ABNAHAUSA