Gwamnatin Ireland tana shirin bayar da sanarwar amincewarta da yankin Falasɗinu a matsayin ƙasa mai ‘yancin kanta, duk da yake Isra’ila ta yi matuƙar adawa da wannan matakin, a cewar wata majiya da ke da masaniya game da lamarin.
Ƙasashe mambobin Tarayyar Turai da suka haɗa da Ireland, Sifaniya, Slovenia da Malta a makonnin baya bayan nan sun bayyana aniyarsu ta amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa, wataƙila a taron haɗin-gwiwa, suna masu cewa bai wa yankin na Falasɗinu ‘yanci shi ne kaɗai zai kawo dauwamammen zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Wannan yunƙuri na zuwa ne a yayin da Isra’ila ke ƙara shan matsin lamba daga ƙasashen duniya domin ta daina kisan kiyashin da take yi a Gaza.
Tun shekarar 1988, ƙasashe 139 cikin 193 mambobin Majalisar Ɗinkin Duniya sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin kanta.
Gwamnatin Ireland ta ce matakin da za ta ɗauka na amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa zai ƙara ƙaimi a yunƙurin tabbatar da zaman lafiya da kuma samun ƙasashe biyu kowace mai ‘yancin kanta.
Norway ta ce ‘wajibi’ ne ta kama Netanyahu idan ICC ta bayar da umarni
Norway ta zama ƙasa ta farko ta Turai da ta bayar a sanarwar cewa za ta kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaronsa Yoav Gallant idan Kotun Hukunta Masu Aikata Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ta tabbatar da sammacin kama su.
Ministan Harkokin Wajen Norway Espen Barth Eide ya ce idan aka gabatar da sammacin kama Netanyahu da Gallant a madadin Kotun da ke Hague, za su bi umarninta na kama su idan mutanen biyu suka je Norway.
DUBA NAN: Kotun Duniya Ta Fara Sauraron Shari’a Kan Hare Haren Isra’ila A Rafah
Wata jaridar ƙasar Norway da ake wallafawa a shafin intanet Eide ta tabbatar da cewa Netanyahu zai fuskanci yiwuwar a miƙa shi ga kotun idan ya je ƙasar Norway