Iraqi Jiragen Yakin Turkiyya Sun Yi Luguden Wuta Kan Tsaunukan Yankin Kudawan Kasar.
Jiragen yakin kasar Turkiyya sun yi luguden wuta kan wasu yankuna a cikin lardin Kurdistan na kasar Iraqi da sunan yaki da ‘yan kungiyar PKK wato kurdawa masu son ballewa daga kasar ta Turkiyya wadanda suke samun mafaka a yankin.
Kamfanin dillancin labaran ‘Almalumah’ na kasar Iraqi ya nakalto wasu wadanda suka ganewa idanunsu hare-haren na jiya Lahadi a cikin yankin tsaunuka na Koreh, yana cewa hare haren sun fada kan wani gidan mai da wasu gonaki a yankin amma babu rahotannin rasa rai ko guda.
Sojojin Turkiyya sun sha kai irin wadannan hare-haren a yankin ba tare da tuntubar gwamnatin kasar Iraqi ba. Wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Sannan ya sabawa dokokin kasa da kasa wadanda suke haka take huruwan wata kasa ba tare da izininta ba.