Iran; Taron Astana Zai Maida Hankali Kan Batun Siriya, Ukraine, Da Matsalar Abinci.
A Iran, an fara taron Astana karo na bakwai, wanda shugabannin kasashen Rasha, Turkiyya da Iran ke halarta.
Taron bisa ga al’ada wata haduwa ce ta tsakanin kasashen uku domin tattauna batutuwan da suka shafi kasar Siriya, saidai a wannan karon da alama rikicin Ukraine da kuma matsalar abinci dake addabar duniya zasu fi mamaye taron.
Akwai yiwuwar shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyib Erdogan su tattauna kan yadda za’a fitar da hatsin Ukraine a tattaunawar da zasuyi ta kud-da-kud karon farko tun bayan da Rasha ta abkawa Ukraine.
Karon na biyu kuma kenan da Putin ya fida daga kasarsa zuwa wata kasa tun bayan soma yaki da Ukraine.
READ MORE : Jagora; Kai Hari A Arewacin Siriya Zai Iya Cutar Da Turkiyya Da ma Yankin.
Shugaban kasar Iran mai karbar bakuncin taron,Ibrahim Ra’isi, zai gana da takwarorin nasa inda zasu tattauna kan alakokin dake tsakaninsu.
READ MORE : Iran Ta Zargi Amurka Da Tada Rikice Rikice A Gabas Ta Tsakiya.
READ MORE : Iran; Amurka Na Kokarin Haifar Da Rikici A Yankin Yammacin Asiya.
READ MORE : Kuwait; Cibiyoyi 28 Sun Fitar Da Bayani Na Nuna Aadawa Da Duk Wani Mataki Na Kulla Alaka Da Isra’ila.