Iran Tace Har yanzu Bata Ga Martanin Amurka Kan Tattaunawar Vieana Ba.
Da yake ishara game da ziyarar da mai shiga tsakani na kungiyar tarayyar turai ya kai Enrique Mora ya kawo nan birnin Tehran kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Saed Khatib Zade ya ce sakon da Iran ta mikawa Mora a fili yake , kuma muna shirin daukar mataki amma yazuwa yanzu babu wani sako da aka samu daga kasar Amurka.
Matsalar da aka samu a tattaunawar Vieanna ta samo asali ne daga matakin da Amurka ta dauka na kasa yanke shawara kan sauran batutuwan da suka rage , don haka ba zamu ci gaba da jira ba har abada , don haka ya zama wajibi Amurka ta yanken matakinta na siyasa akan batun.
READ MORE : Amurka Na Sanya Ido Kan Kisan Da Ake Yi A Mali.
Da yake tsokaci game da Ayyukan Diplomasiya da Ma’aikatar ta yi a shekarar da ta gabata, na kalubalantar takunkumin da aka kakaba mata da habaka kasuwanci a bangaren masu zaman kansu da na jama’a da sayar da man fetur da sauran kayan dab a na mai ba an cimma kyakkyawar matsaya.
READ MORE : Rusesabagina – Kotun Rwanda Ta Amince Da Daurin Shekaru 25 Kan Tauraron Fim.