A ranar lahadi 17 July 2022 fadar gwamnatin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran dake babban birnin Tehran ta zargi gwamnatin amurka da ayyukan tada zaune tsaye gami da samar da rikice rikice a yankin gabas ta tsakiya.
Hakan na zuwa kwana daya bayan shugaban kasar amurka Joe Biden ya kammala ziyara a yankin na gabas ta tsakiya inda ya gana da shugabannin wasu kasashe a kasar Saudiyya, kuma ya bayyana aniyar sa ta cigaba da bada goyon bayan sa ga haramtacciyar kasar Isra’ila wacce ke gallazawa raunanan falasdinawa tare da mamaye yankunan su.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Nasser Kanani ya bayyana cewa, dama amurka ta tabbatar da cewa farfagandar kin jinin Iran data aiwatar batayi nasara ba saboda haka yanzu zata mayar da hankali kana tayar da rikice rikice a yankin na gabas ta tsakiya domin hana Iran din damar aiwatar da manufofin ta cikin lumana.
A ziyarar sa shugaba biden yayi wasu kalaman tunzuri inda yake bayyana cewa, ba zasu bar wata kasa a yankin na gabas ta tsakiya tayi tasiri a kana wata ba ko ta hanyar siyasa, diflomasiyya ko kuma karfin soji, a wanin salon gugar zana wanda yake nuna ga Iran.
Ziyarar biden gabas ta tsakiya na farko na zuwa ne a dai dai lokacin daya rage ‘yan kwanaki Shugaban Kasar Rasha Vladimir Putin ya ziyarci Tehran babban birnin Iran din a ranar 19 ga july na shekarar da muke ciki (2022).
Shugaban amurka joe biden a wani jawabi daya gabatarwa shugabannin kasashen larabawan da suka samu halarta a birnin jeddah na saudiyyab ya bayyana cewa amurka zata cigaba da katsalandan a lamuran gabas ta tsakiya.
”Ba zamu tafi mu bar Chaina, Rasha ko Iran su maye gurbin mu ba” a ta bakin biden.
Wannan shine barazana mafi girma da biden yayi a yayin ziyarar tasa zuwa yankin gabas ta tsakiya mai fama da katsalandan din bakin turawan yamma.