Jamhuriyar musulunci ta Iran ta aike da taimako zuwa kasar Siriya, Kasar dake fama da rkice rikice tattare da tashin hankalin girgizar kasar mai karfin gaske da ya faru a wasu yankuna na kasar.
Kamar yadda Press T.v ta rawaito mashawarcin al’adun Iran din a babban birnin Damascous na Siriya Alireza Fadavi ya bayyana cewa jirgin taimakon karo na shida ya sauka a filin sauka da tashin jirage na Latakia a ranar juma’a.
Latakia yace wannan shine jirgi na uku wanda ya saka a filin sauka ta tashin jirage na Latakia, ambasadan yace, wannan taimako karo na shida ya kunshi ton 19 na kayan taimako, ton 5 na dabino, kayan kula da jarirai katan 269, ton 5 na shinkafa, katifa guda 500, tantuna 90 da kuma kayan abinci.
Tuni Iran ta aike da jirage cargo guda biyu dauke da kayan taimako zuwa birnin Damascous, guda biyu kuma zuwa birnin Aleppo a kokarin ta na taimakon wadanda girgizar kasar ta rutsa dasu.
Rahotanni na baya bayan na da suka zo hannu sun bayyana girgizar kasar tayi sanadin mutuwar fiye da mutum dubu ashirin a Turkiyya da Siriya.
Masu ceton gaggawa daga kasashe mabambanta na ta kokari a tsawon lokaci domin ceto masu sauran lunfashi daga karkashin baraguzai.
Iran kuma ta bayyana cewa, ta shirya tsaf domin aikewa ta taimakon zuwa wasu garuruwan da abin ya shafa ciki har da garin Idlib wanda ke karkashin ikon kungiyoyin tsageru.
Ministan harkokin wajen Iran Amir Abdollahian ne ya bayyana hakan a tattauwar wayar tarho da ta gudana tsakanin sa da shugaban kwamitin kasa da kasa na Red Cross (ICRC) Mirjana Spoljaric Egger a ranar alhamis.
Ya kuma bayyana shirinn Iran na taimakawa wadanda girgizar kasar ta shafa a kasashen Siriya da Turkiyya, ya kuma bayyana cewa tuni sun aike da taimako zuwa kasashen biyu kuma ya bayyana cewa kasar sa a shirye take ta karbi wadanda suka ji rauni a girgizar kasar a asibitocin ta.