A ranar lahadi 13 ga watan fabrairun 2022 din da muke ciki ne ma’aikatar tsaron Iran bisa jagorancin dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar suka kaddamar da sabbin makamai kirar zamani kuma kirkirar cikin gida guda goma.
Makaman wadanda aka tabbatar masu cin nisan zango ne an kaddamar dasu tare da halartar manyan baki daga bangaren tsaron kasar ciki har da ministan tsaron kasa janaral muhammad reza ashtiani.
Kaddamar da makaman da gwamnatin ta Iran tayi na cikin bukukuwan zagayowar ranar cika shekaru 43 da nasarar juyin juya halin musulunci na Iran din wanda Ayatullah Ruhullah Musawi Khumaini ya jagoranta.
Makaman da aka kaddamar dai sun hada da manyan makamai masu linzami, jiragen yaki gami da alburusai masu cin nisan zango ba irin wadanda aka saba gani yau da kullum ba.
Kasar Iran dai na zaman kasa mafin karfin soji a nahiyar asiya kuma ta shahara da takaddama tsakanin ta da kasar amurka da kuma wasu daga cikin kasashen yammacin turai dama haramtacciyar kasar Isra’ila.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an fara samun sabani tsakanin Iran da amurka tun shekaru 43 da suka gabata lokacin da Iraniyawa suka gabatar da juyin juya hali kuma suka fatattaki gwamnatin sarki shah wanda ke samun goyon bayan amurkan kuma aka samar da sauyin tsari a kasar inda gwamnatin gurguzun ‘yan kishin kasa ta karbi iko, tasirin amurka kuma ya zama babu shi a kasar.
Tarihi ya tabbatar da cewa amurka da kawayen ta sunyi kokarin kawo karshen sabuwar gwamnatin ta Iran tun shekaru 43 da suka gabata inda ta hada kai da suran kasashe suka marawa saddam hussain shugaban kasar Iraki na wancan lokaci inda akayi yakin shekaru takwas kafin jamhuriyar musulunci ta Iran ta samu nasara amma tun loakcin babu dadi tsakanin gwamnatocin amurka dana Iran din, zuwa yanzu Iran ta mallaki makamai masu tarin yawa gami da karfin soji wanda hakan ya bada daman zama kasa mafi karfin soji a nahiyar asiya